Imo: Shugaban PDP Ya Sauka Daga Kujerarsa, Ya Fice Daga Jam’iyya da Magoya Bayansa

Imo: Shugaban PDP Ya Sauka Daga Kujerarsa, Ya Fice Daga Jam’iyya da Magoya Bayansa

  • Jam'iyyar PDP a jihar Imo tana fuskantar babban kalubale yayin da shugaban jam'iyyar na jihar Cif Charles Ugwu ya yi murabus
  • Ba iya Cif Ugwu ne kadai ya fice daga jam'iyyar ba, kusan dukkanin manyan jiga-jigan PDP a jihar sun hakura da zama a jam'iyyar
  • Murabus din shugaban jam'iyyar tare da dumbin magoya baya ba zai rasa nasaba da ficewar tsohon gwamnan jihar daga jam'iyar ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Imo - Shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Imo, Cif Charles Ugwu ya yi murabus daga mukaminsa da kuma ficewa daga jam’iyyar gaba daya.

Shugaban jam'iyyar PDP a jihar Imo ya yi murabus
Imo: Shugaban PDP, Cif Charles Ugwu da magoya bayansa sun fice daga jam’iyyar. Hoto: @DEagleOnline
Asali: Twitter

Ficewar Ihedioha ta bar kura a PDP

Murabus din Ugwu na zuwa ne kwanaki bayan da tsohon gwamnan jihar Emeka Ihedioha ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar, jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kwanakin PDP za su zo karshe, tsohon ɗan Majalisar Tarayya ya sake ficewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga Ugwu, sauran jiga-jigan jam’iyyar da suka fice daga PDP a Imo sun hada da tsohon mataimakin gwamna, Injiniya Gerald Irona.

Tsohon shugaban jami'ar fasaha ta tarayya da ke Owerri kuma tsohon kwamishinan ilimi na jihar, Farfesa Jude Njoku shi ma ya fice daga jam'iyyar.

Sauran sun hada da tsohon dan majalisa, Ikenga Mayor Eze; tsohon shugaban ma'aikata, Dr. Vin Udokwu da shugaban matasan jam'iyyar PDP na jihar, Evang Anozie Udenwa.

An samu karin masu murabus a PDP

Jaridar The Cable ta rahoto dan takarar majalisar dokokin jihar daga Ikeduru, Bar. Sonny-Unachukwu John da dan takarar majalisar jihar daga Isiala Mbano, Pius Omah sun yi murabus.

Sauran sun hada da tsoffin kwamishinoni, Engr Sly Enwerem da Hon Cif Nkiruka Ibekwe Esq, da Cif Sir Martin Opara (Ikemba), Cif Mrs Ann Njoku, Chief Angus Okorie da Cif Edward Uzoechila Ezeh.

Kara karanta wannan

PDP ta sake samun nakasu bayan tsohon gwamna ya yi murabus, an rasa jiga-jigai 8

Manyan jiga-jigan PDP da suka yi murabus sun hada da sakataren jam'iyyar na shiyyar Owerri, Hon Cif Ben Mere; Sakataren shiyyar, Prince Macdonald Enwerem da Chibuike Paschal Maduike da Hon. Ike Uche.

Emeka Ihedioha ya fice daga PDP

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Imo, Rt. Hon. Emeka Ihedioha ya hakura da zama a PDP, ya fice daga jam'iyyar.

Kamar yadda Ihedioha, wanda tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai ne, ya ce PDP ta sauka daga turbar da ya san jam'iyyar tun shekaru 26 baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel