"Babban Abinda Zan Yi Kewa Sosai Bayan Na Sauka Mulki", Shugaba Buhari

"Babban Abinda Zan Yi Kewa Sosai Bayan Na Sauka Mulki", Shugaba Buhari

  • Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana muhimmin abinda zai yi kewa idan ya bar kan madafun ikon ƙasar nan
  • Shugaba Buhari ya ce zai yi kewar mutanen kirkin da ya yi aiki tare da su na tsawon shekara takwas a gwamnatinsa
  • Shugaban ƙasar na ta shirye-shiryen yin bankwana da madafun ikon ƙasar nan a ranar 29 ga watan Mayun 2023

Abuja - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana babban abinda zai yi kewa sosai bayan ya miƙa mulki ga sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa, shugaba Buhari ya ce bayan ya bar mulki zai yi kewar mutanen da ya yi aiki tare da su a gwamnatinsa, waɗanda ya kira da mutanen kirki.

Shugaba Buhari ya bayyana abinda zai yi kewa bayan ya sauka mulki
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari Hoto: Thisdaylive.com
Asali: UGC

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a birnin Landan, UK a cewar hadiminsa na musamman kan watsa labarai, Femi Adesina.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Da Ya Lashi Takobin Yaƙar Tinubu a Majalisa Ta 10 Ya Gana da Buhari, Bayanai Sun Fito

A kalamansa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A birnin Landan sati biyu da suka gabata, da ni da sauran ƴan jaridar fadar gwamnati, mun tambayi shugaban ƙasa abinda zai yi kewa sosai idan ya sauka daga mulki."
"Ya ba mu amsa da cewa zai yi kewar mutanen kirkin da ya yi aiki tare da su a shekara takwas da suka gabata, kamar wasu daga cikin mu da ke a wajen."

Na sauke nauyin da aka ɗora min - Adesina

Da ya ke magana kan aikin da ya yi, Adesina ya ce ya hidimtawa shugaban ƙasar iyakar iyawarsa, sannan zai bar Villa a matsayin wanda ya samu cikakkiyar gamsuwa na sauke nauyin da aka ɗora masa, cewar rahoton PM News.

"Aiki na ya ƙare, na tattara ƴan jakunkuna na sannan na shirya barin Villa. Lokacin da zan fice daga fadar shugaban ƙasa a ranar Juma'a 26 ga watan Mayun 2023, shine zai zama na ƙarshe a matsayin ɗan cikin gida. Idan har na ƙara dawowa, sai dai a matsayin baƙo wanda ya kawo ziyara." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: "Shugaban EFCC Ya Nemi Cin Hancin $2m Daga Wuri Na," Gwamnan APC Ya Fasa Ƙwai

An Kasje Sama Da N500m Don Siyen Littafin Shugaba Buhari

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa manyan ƴan siyasa da hamshaƙan attajirai na ƙasar nan sun yi facaka da naira wajen siyan littafin shugaba Buhari.

Asiwaju Bola Tinubu, Dangote da Abdulsamad Rabiu BUA, na daga cikin waɗanda suka siya kwafin littattafan da aka wallafa domin shugaba Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel