Korar Sanata Goje Daga Jam'iyyar APC: Uwar Jam'iyya Ta Raba Gardama

Korar Sanata Goje Daga Jam'iyyar APC: Uwar Jam'iyya Ta Raba Gardama

  • Jam’iyya mai mulki ta APC a matakin kasa ta ce sanata Muhammad Goje cikakken dan jam’iyyar ne
  • Wannan na zuwa ne bayan jam’iyyar ta kori sanatan a matakin gundumomi da kuma jiha a watan Afrilu
  • Kakakin jam’iyyar, Felix Morga ya tabbatar da cewa sanatan cikakken dan jam’iyyar ne a kowane mataki

Abuja - Jam’iyya mai mulki ta APC a matakin kasa ta ce Sanata Muhammad Danjuma Goje cikakken dan jam’iyyar ne kuma bai koru ba.

Jam’iyyar ta bayyana haka ne dangane da korar da aka yi wa tsohon gwamnan jihar kuma sanatan Gombe ta tsakiya, Muhammad Danjuma Goje a matakin karamar hukuma a watan Afrilu na wannan shekara.

Goje/APC
Sanata Goje Cikakken Dan APC Ne. Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar a shafinta na Twitter ta bakin kakakin ta, Felix Morga ta bayyana cewa wannan mataki da jam’iyyar da ta dauka a matakin jiha bai inganta ba har sai zuwa lokacin da jam’iyyar za ta gama bincikenta.

Kara karanta wannan

Wallahi Ko a 2019, Abba Gida Gida Ya Ci Zaben Gwamnan Kano - 'Yar APC Ta Fasa Kwai

Ana zargin sanata Goje da yi wa jam’iyyar zagon kasa a zabubbukan da aka gudanar daban-daban a watan Faburairu da Maris na wannan shekara, jaridar TheCable ta tattaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Zargin da ake yi wa Sanata Goje

Shugaban jam’iyyar gundumar Kashere dake karamar hukumar Akko a cikin jihar, Tanimu Abdullahi ya kori sanatan a watan Afrilu daga jam’iyyar bisa zargin hada kai da jam’iyyun adawa a jihar da kuma zagon kasa wa jam’iyyar APC.

A cikin sanarwar, Felix Morga ya ce:

“Mun samu wani rahoto dake yawo a kafar sada zumunta cewa an sallami sanata Muhammad Danjuma Goje daga jam’iyyar APC a matakin jiha.
“Jam’iyyar mu tana bada umarnin cewa korar da akayi da duk wani abin da ke da alaka da shi a ajiye shi a gefe, har sai kwamitin tsare-tsare ta jam’iyyar ta gama binciken ta akai.”

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Yi Amai Ta Lashe Ta Soke Dakatarwar Da Ta Yi Wa Wasu Jiga-Jiganta a Jihar Benue

Sanarwar ta kara da cewa:

“Saboda haka, sanata Goje cikakken dan jam’iyyar APC ne a matakin jiha dama kasa baki daya.”

Jam'iyyar APC a Matakin Jiha Ta Kori Sanata Goje Daga Jam'iyyar

A wani labarin, jam'iyyar APC a matakin jiha ta kori sanata Danjuma Goje bisa zargin zagon kasa wa jam'iyyar a zabukan da suka gudana.

Jam'iyyar a matakin gunduma ta kori sanatan ta bakin shugabanta Tanimu Abdullahi kan zargin hada kai da jam'iyyun adawa a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel