Jam'iyyar APC Ta Soke Dakatarwar Da Aka Yi Wa Sanata Barnabas Gemade Da Wasu Mutum Biyar a Benue

Jam'iyyar APC Ta Soke Dakatarwar Da Aka Yi Wa Sanata Barnabas Gemade Da Wasu Mutum Biyar a Benue

  • Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi amai ta lashe kan dakatarwar da ta yi wa wasu jiga-jiganta a jihar Benue
  • Uwar jam'iyyar ta ƙasa itace ta soke dakatarwar da aka yi wa sanata Barnabas Gemade, Farfesa Terhemha Shija da wasu mutum biyar a jihar
  • Jam'iyyar tace har yanzu su halastattun ƴaƴan jam'iyyar ne zuwa lokacin da kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar zai kammala nazarinsa kan lamarin

Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta soke dakatarwar da aka yi wa sanata Barnabas Gemade, Farfesa Terhemha Shija da wasu mutum biyar a jihar Benue, rahoton TVC News ya tabbatar.

Kwamitin zartaswar jam'iyyar na jihar Benue ne dai ya dakatar da su, bisa zarge-zargen cin dunduniyar jam'iyyar a lokacin zaɓe.

APC ta soke dakatarwar da aka yi wa Barnabas Gemade a Benue
Sanata Barnabas Gemade Hoto: Premiumtimes.com
Asali: UGC

Sai dai jam'iyyar a wata sanarwa da kakakinta na kasa, Felix Morka, ya fitar ta bayyana cewa ta jingine dukkanin matakin da aka ɗauka dangane da lamarin har sai zuwa lokacin da kwamitin gudanarwar jam'iyyar na ƙasa (NWC), zai kammala nazarinsa kan lamarin.

Kara karanta wannan

Kwamitin Aikace-Aikacen APC Na Ganawa Da Sanatoci Kan Matsalolin Da Suka Tunkaro Jam'iyyar

Felix Morka ya bayyana cewa har yanzu, sanata Gemade da sauran waɗanda aka dakatar, halastattun ƴan jam'iyyar APC ne, cewar rahoton Premium Times.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar na cewa:

"Hankalin hedikwatar jam'iyyar APC ya kai kan rahoton dakatar da sanata Barnabas Gemade, Farfesa Terhemha Shija da wasu mutum biyar da kwamitin zartaswa na jam'iyyar mu a jihar Benue, ya yi."
"Jam'iyya na bayar da umurnin jingine wannan dakatarwar da duk wani abu da ya shafi lamarin, har sai zuwa lokacin da kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar ya kammala nazarinsa akan lamarin."
"A saboda haka, sanata Barnabas Gemade, farfesa Shija da sauran mutum biyar ɗin da aka dakatar, har yanzu halastattun mambobin jam'iyyar mu ne a jihar Benue."

Tsaffin 'Yan Majalisar APC Sun Marawa Takarar Akpabio Da Barau Baya

Kara karanta wannan

Rikicin Jam'iyya: An Dakatar Da Tsohon Shugaban PDP na Ƙasa? NWC Ta Yi Bayani Kan Hukuncin

A wani labarin na daban kuma, tsaffin ƴan majalisar jam'iyyar APC, sun nuna goyon bayan su ga takarar kujerar shugabancin majalisar dattawa ta sanata Akpabio da Barau.

Shugaban ƙungiyar tsaffin ƴan majalisar, Babangida Nguroje, ya bayyana cewa ƴan takarar sun cancanci su ja ragamar shugabancin majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel