Gbajabiamila Ya Ce Ya Yi Nadamar Goyon Bayan Tambuwal Da Ya Yi Ya Zama Kakakin Majalisa

Gbajabiamila Ya Ce Ya Yi Nadamar Goyon Bayan Tambuwal Da Ya Yi Ya Zama Kakakin Majalisa

  • Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa ya yi nadamar goyawa Tambuwal baya ya zama kakakin majalisar a shekarar 2011
  • Gbajabiamila ya bayyana hakan ne a wajen wani taro na 'yan majalisu da jam'iyyar APC ta gudanar ranar Laraba a Abuja
  • Ya kuma nuna goyon bayansa ga dan takarar shugabancin majalisar da jam'iyyar ta tsaida, wato Tajuddeen Abbas

Abuja - Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce ya yi nadamar jagorantar wani gangami da ya yi sanadiyar zamowar Aminu Tambuwal shugaban majalisar wakilai ta 7, jaridar Punch ta wallafa.

A yanzu haka dai Tambuwal shine Gwamnan Sokoto mai barin gado kuma zaɓaɓɓen sanata.

Gbajabiamila/Tambuwal/Majalisar Tarayya
Femi Gbajabiamila ya ce ya yi nadamar oyon bayan Tambuwal ya zama kakakin majalisa. Hoto: The Punch, Pulse NG
Asali: Facebook

Na yi nadama

"Na yi nadama," in ji Gbajabiamila a yayin da ya ke tunawa da irin bijirewar da masu neman kujerar kakakin majalisar suka yi a baya na yin adawa da zaɓaɓɓun 'yan takarar jam'iyyunsu.

Kara karanta wannan

APC Ta Yi Kuskure: An Bayyana Ɗan Cikin Gwamnatin Buhari Da Zai Iya Kawo Sauyi Mai Kyau a Najeriya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban majalisar ya yi wannan jawabi ne da yammacin ranar Laraba a Abuja, a wani taro na haɗin guiwa tsakanin zaɓaɓɓun 'yan majalissun jam'iyyar APC mai mulki da na 'yan adawa.

Dukkansu dai sun amince da ’yan takarar da aka zaba na jam’iyyar APC a matsayin shugaban majalisar wakilai da mataimakinsa, wato Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu, a majalisar wakilai ta 10.

Gabanin Gbajabiamila ya yi magana, dan takarar shugabancin majalisar dattawa na jam’iyyar APC, Sanata Godswill Akpabio ne ya rako shi wurin taron, sannan ya yi ɗan takaitaccen jawabi sannan sai ya fice.

Gbajabiamila ya goyi bayan Tajuddeen Abbas

This Day ta ruwaito cewa a wajen taron, Femi Gbajabiamila ya bayyana goyon bayansa ga ɗan takarar da jam'iyyar APC ta tsaida wato Tajudeen Abbas.

Ya ce ya bayyana goyon bayan nasa ga Tajudeen ɗin ne domin fatan zai ci-gaba a kan irin nasarorin da ya samu a lokacin shugabancinsa.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Yi Fatali da Shirin Gwamnonin Arewa 5, Ya Faɗi Wanda Yake Goyon Baya a Majalisa Ta 10

Wannan ne dai karo na farko da Gbajabiamila ya yi magana a bainar jama'a dangane da 'yan takarar da jam'iyyar ta su ta APC ta tsayar.

Taron dai ya gudana ne jiya Laraba, 17 ga watan Mayu, a Otel ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja. Ya samu halartar 'ya 'yan jam'iyyar ta APC da dama.

Peter Obi ya gaza biyan N1.5m don karbar takardu

A wani labarin na daban kuma, dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi, tare da jam'iyyarsa sun gaza biyan kudi N1.5m don karbar wasu takardun zabe da suke so su gabatar a gaban kotu.

Lauyan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Abubakar Mahmoud ne ya shaidawa kotu hakan a yayin da yake maida martani kan ikirarin da lauyan Obi ya yi na cewar an hana su wasu takardu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel