Labour Da Peter Obi Sun Gaza Biyan N1.5m Don Karɓar Takardun Da Kotu Ke Nema, INEC

Labour Da Peter Obi Sun Gaza Biyan N1.5m Don Karɓar Takardun Da Kotu Ke Nema, INEC

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta musanta zargin da jam'iyyar Labour da ɗan takararta Peter Obi ke yi na cewar an hana su kayayyakin zaɓe
  • Lauyan INEC Abubakar Mahmoud ne ya shaidawa kotu hakan, inda ya ce sun ƙi su biya N1.5m domin a ba su takardun da suke buƙata
  • Lauyan jam'iyyar APC, Lateef Fagbemi ya ce shi ma yana goyon bayan hukumar zaɓen kan batun takardun da ake nema

Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta ce jam’iyyar Labour da ɗan takararta Peter Obi, sun ƙi biyan N1.5m da aka nema domin a basu takardun da suke nema.

Lauyan INEC Abubakar Mahmoud ne ya shaidawa kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa haka a ranar Laraba, kamar yadda yake a rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

"Tinubu Ba Zai Wuce Wata 6 Zuwa 7 a Kan Kujerar Shugaban Ƙasa Ba," Babban Jigo Ya Faɗi Abinda Zai Faru

Peter Obi
INEC Ta Ce Jam'iyyar Labour da Peter Obi Sun Gaza Biyan N1.5m Don Karɓar Takardun Da Kotu Ke Nema. Hoto: Arise TV
Asali: UGC

Mahmoud na mayar da martani ne kan iƙirarin da Levy Uzoukwu lauyan jam’iyyar Labour da ɗan takararta suka yi.

Sun ce hukumar ta INEC ta ƙi fitar da wasu muhimman takardu da suka buƙaci a gabatar dasu a matsayin shaida a ƙarar da suka shigar a gaban kotu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

INEC ta ƙi ta saki kaso 70 cikin 100 na takardun

Uzoukwu ya shaidawa kwamitin mutane biyar na kotun ƙarƙashin jagorancin Haruna Tsammani, cewa INEC ta ƙi ta saki 70% na takardun zaɓen da ake nema.

Uzoukwu ya ce musamman ma dai takardun da suka shafi zaɓen jihohin Ribas da na Sokoto, har yanzu sun ƙi samuwa.

INEC na neman kudi, inji lauyan Obi

Dangane da jihar Sokoto, Uzoukwu ya ce jami’an INEC sun buƙaci a biya su kuɗi N1.5m kafin samun damar karɓar takardun.

Kara karanta wannan

Rigima Sabuwa: Shugaban Tsagin Jam'iyyar Labour Party Ya Sha Da Kyar a Kotun Zabe, Bidiyon Ya Bayyana

A cewarsa:

"Misali ƙaramin kwamishinan zaɓe a jihar Rivers, ya ce mana ba su da fom ɗin EC8A da za su ba mu."

Mun turawa INEC saƙonni har sau biyar

Lauyan ya ƙara da cewa an aikawa INEC wasiƙu har biyar tare da umarnin da kotu ta bayar a ranakun 3 da 8 ga watan Maris na cewar su bai wa masu ƙorafe-ƙorafen damar duba kayayyakin zaɓe da suka dace tare da damar yin kwafin su.

Da yake mayar da martani kan zargin, lauyan INEC ya ce lauyoyin Peter Obi sun ƙi halartar taron da aka shirya yi domin tattauna batun takardun da za a gabatar gaban kotu.

A cewarsa:

“Mun yi cewa za mu haɗu a ranakun Litinin da Talata 15 da 16 ga watan Mayu kan maganar takardun. Amma a ranar Litinin, 15 ga watan Mayu, aka kirani ake shaida min cewa lauyoyin jam’iyyar Labour ba su zo wurin da ake taron ba.”

Kara karanta wannan

APC Ta Yi Kuskure: An Bayyana Ɗan Cikin Gwamnatin Buhari Da Zai Iya Kawo Sauyi Mai Kyau a Najeriya

Sakon da lauyoyin Obi suka kai wa INEC

A rahoton da jaridar Leadership ta yi, lauyan INEC ya ce lauyan jam'iyyar Labour ya aiko musu da saƙo, inda yake shaida musu cewa mutanen da ya yake karewa ba su shirya biyan N1.5m dangane da takardun na Sokoto ba.

Ya ce sun bai wa jam'iyyar ta Labour wasu takardun zaɓe na Rivers, amma suka ce sai dai a basu duka takardun.

A nasa ɓangaren, lauyan jam'iyyar APC, Lateef Fagbemi, ya ce shi ma ya na tare da INEC kan batun takardun.

Doguwa ya janyewa Tajuddeen Abbas

A wani labarin kuma, shugaban Masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya sanar da janyewarsa daga cikin masu neman shugabancin majalisar ta wakilai.

Haka nan ya sanar da marawa ɗan takarar da jam'iyyar APC ta tsaida wato Tajudeen Abbas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel