Jerin Sunayen Manyan ‘Yan Siyasa, Malaman Addini, Da Sauran Waɗanda Ba Su Son a Rantsar Da Tinubu Ya Bayyana

Jerin Sunayen Manyan ‘Yan Siyasa, Malaman Addini, Da Sauran Waɗanda Ba Su Son a Rantsar Da Tinubu Ya Bayyana

A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu ne za a rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da mataimakinsa Kashim Shettima.

Za a yi bikin rantsar da shugaban ƙasar ne a dandalin Eagle Square da ke Abuja, kuma shugabannin duniya da sauran manyan baƙi za su halarci taron mai ɗumbin tarihi a Najeriya.

Mun tattaro muku jerin sunayen waɗanda ba sa son Buhari ya miƙawa Tinubu mulki a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa.

Sunayen 'yan siyasa da ba su so a rantsar da Tinubu
Wasu manyan yan siyasa da fastoci ba su so a rantsar da Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: UGC

Mafi yawancinsu fitattun mutane ne, jiga-jigan jam’iyyu da ma ƙungiyoyi da dama da suka yi kira kan a dakatar da bikin rantsar da Tinubu; bisa hujjarsu ta cewa tun da an shigar da ƙararsa a kotu, bai kamata a rantsar da shi ba har sai an ƙarƙare shari'a.

Sai dai kuma gwamnatin tarayyar Najeriya, ƙarƙashin jagorancin shugaba Muhamamdu Buhari na jam'iyyar APC, ta tsayu kan cewa rantsar da Tinubu a 29 ga watan Mayu na nan babu fashi.

Kara karanta wannan

Rantsar Da Tinubu: Muhimman Abubuwa 3 Da Yakamata Ku Sanya Ido Akai a Ranar 29 Ga Watan Mayu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gabanin babbar ranar da take ƙaratowa nan da ‘yan sa’o’i kaɗan, Legit.ng ta tattaro cikakkun jerin sunayen manyan ‘yan siyasa, fastoci masu faɗa aji da sauran mutanen da ba su goyon bayan a rantsar da Tinubu ba. Mutanen su ne kamar haka:

1. Bode George

Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa Cif Olabode George, ɗaya ne daga cikin waɗanda suka fito fili suka nuna rashin goyon bayansu wajen miƙawa Tinubu madafun iko.

Jigon na jam'iyyar PDP, wanda a can baya ya sha alwashin yin hijira idan Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa.

A kwanakin baya, George ya bayyana cewa ranar 29 ga watan Mayu ba dole sai a cikinta ne kaɗai za a iya ƙaddamar da sabuwar gwamnati.

Ya kuma bayyana cewa, har sai an gama warware ƙararrakin da ke gaban kotu ne za a iya rantsar da Tinubu.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Yi Kira Mai Daukar Hankali Ga Atiku Da Peter Obi a Jawabin Bankwana

2. Datti Baba Ahmed

Wani dan siyasar da ba ya son Tinubu ya karɓi mulki daga hannun shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen da ya gabata, wato Yusuf Datti Baba-Ahmed.

Datti yana ganin cewa idan aka rantsar da Tinubu a ranar Litinin, hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ga dimokuraɗiyyar Najeriya ba.

A cewarsa:

"Abin da yake shirin faruwa a ranar 29 ga watan Mayu, rashin bin tsarin mulki ne, na sake maimaitawa, rashin bin tsarin mulki ne.”

3. Cardinal John Onaiyekan

Tsohon babban malamin cocin katolika, Cardinal John Onaiyekan na cikin fitattun ‘yan Najeriyan da ba sa goyon bayan rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

Malamin ya bayyana cewa tun da dai ana ƙalubalantar nasarar zaɓen Tinubu a kotu, ya kamata a dakatar da batun rantsar da shi har sai kotu ta yanke hukunci kan lamarin.

Kara karanta wannan

Yana Dab Da Sauka Mulki, Shugaba Buhari Ya Bayyana Wani Abu Da Ya Faru Da Shi Wanda Bai Taba Tunani Ba

4. Simon Okeke

Dr Simon Okeke, wani fitaccen ɗan siyasa ne a yankin Kudu maso Gabas. Ya buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, da alƙalin alkalan Najeriya da su dakatar da bikin rantsar da Tinubu har sai kotun ƙoli ta yanke hukunci game da ainihin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.

A cewar Okeke, hukuncin na kotun kolin ne ya kamata ya fara zuwa gabanin ƙaddamar da Tinubu.

5. Chief Ambrose Owuru

Tsohon dan takarar shugaban ƙasa, Cif Ambrose Owuru ma ya shigar da ƙara a kotun daukaka ƙara dake Abuja, kan bikin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.

Al’amura dai sun caɓe masa ne a lokacin da kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta ci tararsa naira miliyan 40, saboda ya shigar da ƙara mara dalili a gaban kotu yana neman a dakatar da rantsar da Tinubu.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Ƙarar da Ta Nemi Dakatar da Rantsar da Bola Tinubu

6. Praise Ilemona, Fasto Paul Issac Audu da Dakta Anongu Moses

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta ci tarar Praise Ilemona, Fasto Paul Issac Audu da Dakta Anongu Moses da lauyansu tarar naira miliyan 17, saboda shigar da ƙara ba tare da wani dalili ba, kan neman a dakatar da bikin rantsuwa.

Kotun ta dai ci tarar mutane ukun da suka shigar da ƙarar neman a dakatar da rantsar da Tinubu a matsayin sabon shugaban ƙasa a ranar 29 ga watan Mayu.

Gwamna Masari ya nemi afuwar al'ummar jihar Katsina

A wani labarin mu na baya, gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya nemi afuwar ɗaukacin al'ummar jihar bisa duk wani kuskure da ya yi a shekaru takwas da ya shafe yana mulki.

Gwamnan ya yi roƙon ne a lokacin da yake jawabin bankwana ga al'ummar jihar ta Katsina da ya shugabanta tsawon wannan lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel