Kotu Ta Kori Karar da Wasu Mutum Uku Suka Nemi a Dakatar da Rantsarwa

Kotu Ta Kori Karar da Wasu Mutum Uku Suka Nemi a Dakatar da Rantsarwa

  • Jim kaɗan bayan hukuncin Kotun koli, babbar Kotun tarayya ta yanke na ta hukuncin kan karar da ta shafi Tinubu
  • Alkalin Kotun ya yi fatali da ƙarar wasu mutum uku da suka nemi a dakatar da bikin rantsar da Bola Tinubu
  • A cewar masu karar Tinubu ya zuba ƙarya a takardun haihuwarsa da na shaidar zama dan kasa

Abuja - Babban Kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi watsi da ƙarar da wasu mutane uku suka shigar, inda suka nemi a dakatar da rantsar da zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

Punch ta rahoto cewa masu shigar da ƙarar, sun roki Kotu ta hana bikin rantsar da Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Bola Tinubu.
Kotu Ta Kori Karar da Wasu Mutum Uku Suka Nemi a Dakatar da Rantsarwa Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sun nemi Kotu ta dakatar da bikin rantsuwan ne bisa zargin cewa akwai lauje cikin maɗi a takardun shekarun Tinubu da shaidar zama ɗan ƙasa wanda ya miƙa wa hukumar zabe INEC.

Kara karanta wannan

Kotun Koli a Najeriya Ta Yanke Hukunci Kan Karar da PDP Ta Nemi a Soke Takarar Tinubu da Shettima

Wane hukunci Kotu ya yanke?

Da yake yanke hukunci ranar Jumu'a, mai shari'a James Omotosho na babbar Kotun tarayya, ya ce mutanen 3, Praise Ilemona Isaiah, Fastor Paul Isaac Audu da Anongu Moses, ba su san me suke yi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin ya ƙara da bayanin cewa mutanen uku ba su da wata tsayayyar manufa kan ƙarar kuma suna kokarin cin mutunci da ɓata lokacin Kotu.

Haka zalika mai shari'a Omotosho ya yanke hukuncin cewa baki ɗaya masu shigar da karar basu da hurumin shigar da ƙara kan batutuwan da suka gabatar.

Ya kuma ƙara da cewa Kotu a karan kanta ba ta da hurumin sauraron ƙarar saboda batu ne da ya shafi zaben shugaban ƙasa, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Daga nan Alkalin ya kori karar kana ya ci masu shigar da ƙara tarar miliyan N10m ga Tinubu, miliyan N5m kuma su baiwa APC da kuma miliyan N1m da lauyan masu kara zai biya duk waɗanda ake ƙara.

Kara karanta wannan

To Fa: Gwamnan Arewa Na PDP Ya Magantu Kan Yuwuwar Ya Koma Jam'iyyar APC

Kotun Koli Ta Yi Watsi da Karar Da PDP Ta Nemi a Soke Tikitin Tinubu da Shettima

A wani labarin kuma Kotun Koli ta yi watsi da Karar da PDP ta nemi a soke tikitin zababben shugaban kasa da mataimakinsa.

Babbar jam'iyyar hamayya PDP ta ɗaukaka kara zuwa Kotun koli bisa zargin cewa Shettima ya tsaya takara biyu a 2023, wanda kuma hakan ya saɓa wa dokar zaɓen Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel