Gwamna Masari Ya Yi Bankwana Ga Katsinawa, Ya Nemi Yafiyar Mutanen Ƙatsina

Gwamna Masari Ya Yi Bankwana Ga Katsinawa, Ya Nemi Yafiyar Mutanen Ƙatsina

  • Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya miƙa ƙoƙon bararsa ga al'ummar jihar domin su yafe masa kurakuran da ya yi
  • Gwamnan ya kuma nuna godiyarsa ga al'ummar bisa halascin da suka yi masa, wanda a cewarsa ba a taɓa yi wa wani ɗan siyasa ba
  • Gwamna Masari ya kuma nuna ƙwarin guiwarsa kan cewa gwamnan da zai gaje shi zai ci gaba da tafiya da jihar kan turbar da ta dace

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya nemi yafiya kan duk wani kuskure da ya yi a shekara takwas da ya yi yana mulkin jihar Katsina, wanda zai zo ƙarshe a ranar Litinin.

A yayin da ya ke bankwana ga al'ummar jihar, ya kuma gode musu bisa abubuwan da suka yi masa, Channels tv ta yi rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Abba Gida-Gida Ya Sha Alwashi Kan Gwamnatin Ganduje, Zai Yi Mata Binciken Kwakwaf

Gwamna Masari ya nemi yafiyar al'ummar jihar Katsina
Gwamna Masari ya nemi yafiyar Katsinawa Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Hakan dai na zuwa ne ƴan sa'o'i kaɗan kafin Masari ya miƙa ragamar mulkin jihar a hannun zaɓaɓɓen gwamnan jihar, Malam Dikko Umaru Radda.

A kalamansa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ni mutum ne kamar kowa, zan yi kuskure, na ga yakamata na zo na nemi yafiya daga wajen al'ummar jihar Katsina.
"Fatan da na ke yi shine su goya masa baya. Roƙon da na ke wajen Katsinawa shine su riƙa ba jihar muhimmanci a dukkanin abinda za su yi."

Gwamnatin Masara ta gudanar da muhimman ayyuka a jihar

Gwamna Masari ya yi amanna cewa ya yi ayyuka da dama waɗanda mutane ba za su gane muhimmancin su ba sai nan da shekara 10 zuwa 20 masu zuwa, inda ya ƙara da cewa dukkanin abinda gwamnatinsa ta yi, domin amfanin mutanen jihar ne.

Kara karanta wannan

"Bana Tsoron EFCC" Gwamnan Arewa Ya Cika Baki, Ya Ce Ba Inda Zai Je Bayan Miƙa Mulki

"Akwai ayyuka da dama waɗanda mu ka aiwatar waɗanda mutane ba za su ga muhimmancin su ba, sai nan da ƙila shekara 10 zuwa 20 masu zuwa."
"Ina godiya ga mutanen jihar Katsina bisa yi min abinda ba a taɓa yi wa wani ɗan siyasa ba a ƙasar nan.

Masari ya kuma nuna ƙwarin guiwarsa kan cewa, gwamna mai jiran gado Dikko Radda, yana da cancantar da zai yi mulki mai kyau a jihar, saboda sanin da ya yi a siyasance na tsawon shekara 20, cewar rahoton Thisdaylive.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wasu mutane daga jihar Katsina, waɗanda suka bayyana ra'ayoyin su dangane da mulkin gwamna Masari.

Wani daga cikinsu mai suna Faisal Sulaiman ya bayyana cewa, babu abinda zai ce dangane da mulkin gwamna Masari, face godiya saboda yadda ya jajirce wajen magance matsalar tsaro a jihar.

A kalamansa:

"A gaskiya babu abinda za mu iya cewa dangane da mulkin Masari face sai dai mu yi godiya, saboda mun san iya yadda ya yi faɗi tashi da kuma wasu lokuta yadda ya hana idanuwan shi barci, ɓangaren yadda za a shawo kan matsalolin tsaro"

Kara karanta wannan

Daga Wurin Taron Miƙa Mulki, Shugaba Buhari Ya Faɗi Jihar da Jirginsa Zai Fara Sauka Kafin Tafiya Daura

Wani mai suna Sahabi Abdulrahman ya bayyana cewa, yankin da ya fito na Katsina ta Kudu basu amfana da komai ba da mulkin Masari, duk da cewa gwamnan ya fito ne daga yankin.

Buhari Ya Ba ‘Yan Najeriya Hakurin Wahalar Da Gwamnatinsa Ta Jefa Su

A wani rahoton na daban kuma, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya nemi yafiya a wajen ƴan Najeriyaa kan wahalar da gwamnatinsa ta jefa su a ciki.

Shugaban ƙasar ya ce ba da son rai bane aka kawo shirye-shiryen da suka gasa ƴan Najeriya, face sai domin kawo ci gaba a ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel