Amurka Za Ta Kakaba Wa ’Yan Najeriya Takunkumin Hana Shiga Cikinta Saboda Raina Dimokradiyya

Amurka Za Ta Kakaba Wa ’Yan Najeriya Takunkumin Hana Shiga Cikinta Saboda Raina Dimokradiyya

  • Amurka ta ce ta samar da tsauraran matakai da za su hana wasu ‘yan Najeriya shiga cikinta nan ba da dadewa ba
  • Magatakardan gwamnatin Amurkan ne ya sanar da haka a shafin gwamnatin kasar a cikin makon nan
  • Ya ce gwamnatin ta saka dokar ne don kara tabbatar da goyon bayanta ga ci gaban dimokradiyya

Abuja - Gwamnatin Amurka ta ce ta dauki tsauraran matakai yadda za su hana wasu daga cikin ‘yan Najeriya shiga kasar da suka kawo wa dimukradiya tarnaki musamman a zaben da aka gundanar a kasar a 2023.

Magatakardan gwamnatin Amurka, Anthony Blinken shi ya bayyana haka a shafin gwamnatin kasar a ranar Litinin 15 ga watan Mayu.

Anthony Blinken/Najeriya
Gwamnatin Amurka Za Ta Hana ’Yan Najeriya da Suke Kawo Cikas Ga Dimukradiya Shiga Kasar, Hoto: Punch
Asali: Facebook

A cewarsa:

“Yau ina sanar muku da cewa mun dauki tsauraran matakai na hana duk wani dan Najeriya shiga kasarmu wadanda suka kawo cikas a dimukradiya a zaben da aka gabatar ta shekarar 2023.”

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Ya Ba Tinubu Shawarwarin Abubuwan da Zai Yi Idan Ya Hau Kan Mulki

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kara da cewa:

“Gwamnatin Amurka za ta dabbaka dimukradiya a Najeriya da sauran kasashen duniya, wannan doka za ta rataya ne kadai akan wasu tsiraru ba wai duka ‘yan Najeriya bane ko kuma gwamnatin kasar.”
“A karkashin sashe na 212 da kuma 3 na doka ta shige da fice, wadannan mutane za a hanasu shiga kasar Amurka a karkashin wata doka su kadai kawai ya shafa wadanda suke kawo cikas ga dimukradiya.”

Ba a bayyana suna ba

Har zuwa lokacin ake tattaro wannan rahoto, gwamnatin Amurkan ba ta bada sunan wani daga cikin wadanda ake maganan akan su ba, cewar jaridar Punch.

Bayanin ya kara da cewa:

“Wadannan mutane da ake magana akansu, sun ci zarafin masu kada kuri’a ta hanyar barazana da kuma sauya sakamakon zabe da sauran ayyuka da suke kawo cikas a dimukradiya.”

Kara karanta wannan

Kaico: Matashi Ya Aika Mahaifiyarsa Kiyama Saboda Sabanin da Suka Samu a Kan ₦10,000

Rahoton Premium Times ta tabbatar cewa Gwamnatin Amurkan ta ce wannan doka da za ta dabbaka zai tabbatar da kokarinta wajen nuna goyon bayanta ga kasar Najeriya wurin ganin kasar ta inganta dimukradiya da bin doka da aiki da shi.

Matashi Ɗan Kano Da Ya Auri Baturiya Ya Shiga Aikin Soja a Amurka

A wani labarin, wani matashi dan jihar Kano, Sulaiman Isah da ya auri Baturiya 'yar Amurka ya shiga aikin soja.

Sulaiman ya wallafa hoton labarin ne a shafinsa na Facebook kamar yadda ya saba dauka sauran abubuwansa a baya, ya godewa ubangiji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel