Abbas da Zababbun Yan Majalisar Tarayya Sun Gana da Shettima a Abuja

Abbas da Zababbun Yan Majalisar Tarayya Sun Gana da Shettima a Abuja

  • Ɗan takarar kakakin majalisar tarayya, Tajudeen Abbas, ya ziyarci zababben mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima
  • Daga cikin tawagar Abbas da suka kaiwa Shettima ziyara harda ɗan takarar mataimakin kakaki, Benjamin Kalu
  • Gamayyar 'yan majalisu na jam'iyyun adawa da suka haɗa kai wuri guda sun halarci taron a gidan Shettima da ke Asokoro

Abuja - Ɗan takarar kujerar kakakin majalisar wakilan tarayya da ake ganin shi ne kan gaba, Tajudeen Abbas, da wasu zababbun yan majalisa sun ziyarci Sanata Kashin Shettima.

Manyan jiga-jigan yan majalisar sun ziyarci zaɓaɓɓen mataimakin shugaban kasa, Kashin Shettima, yayin da ake ci gaba da kace nace a APC kan shugabancin majalisa ta 10.

Kashim Shettima.
Abbas da Zababbun Yan Majalisar Tarayya Sun Gana da Shettima a Abuja Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Honorabul Benjamin Kalu, ɗan takarar mataimakin kakakin majalisar wakilai wanda ya samu goyon bayan jam'iyyar APC ta ƙasa, yana cikkn tawagar da ta ziyarci Shettima.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Yi Hasahen Wanda Zai Samu Nasara a Kotu Tsakanin Tinubu da Atiku, Ya Faɗi Hujja

Jaridar The Nation ta rahoto cewa jim kaɗan bayan isar 'yan majalisar wakilan, suka shiga ganawa da Sanata Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno kuma zababben mataimakin Tinubu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayanai sun nuna cewa da yawan mambobin majalisa na jam'iyyar PDP na cikin mahalarta taron, wanda ke gudana yanzu haka a Ofishin Kashim Shettima da ke Asokoro, Abuja.

Shugaban gamayyar mambobin majalisar tarayya ta 10 na tsagin adawa, Usman Bello Kumo, ne ya jagoranci tawagarsa zuwa wurin taron yau Jumu'a 12 ga watan Mayu, 2023, kamar yadda Tribune ta rahoto.

Baki ɗaya 'yan majalisun jam'iyyun adawa masu alaƙa da ƙunguyar da suka haɗa, sun fara haɗuwa a Stratton Hotel da ke Abuja suka yi kus-kus kafin daga bisa suka zarce wurin Shettima.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa wannan zama na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan 'yan takarar kakaki sun gana da shugaban APC na ƙasa, sun gaya masa korafinsu kan majalisa ta 10.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Atiku Abubakar da Wasu Fitattun Gwamnoni Sun Dira Wurin Liyafa, Bayanai Sun Fito

Buhari da Aisha Sun Koma Gidan Shugaban Kasa Mai Barin Gado

A wani labarin kuma Hajiya Aisha Buhari Ta Tabbatar da Cewa Ita da Buhari Sun Koma Zama a Gidan Shugaba Mai Barin Gado Cikin Aso Villa.

Shugaba Buhari da uwar gidansa, Hajiya Aisha sun fara haramar barin Aso Rock yayin da ranar rantsarwa ke kara matsowa a watan Mayu.

Aisha ta ce ita da mijinta sun koma Glass House, gidan shugaban kasa mai barin gado. Ta ba da shawarin a ci gaba da wannan al'ada a duk lokacin miƙa mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel