Dino Melaye Ya Bayyana Irin Salon Mulkin Da Zai Yi Idan An Zabe Shi Gwamnan Kogi

Dino Melaye Ya Bayyana Irin Salon Mulkin Da Zai Yi Idan An Zabe Shi Gwamnan Kogi

  • Sanata Dino Melaye, dan takarar gwamnan PDP a zaben ranar 11 ga watan Nuwamba ya yi alkawarin ba zai nuna wariyya a gwamnatinsa ba
  • Tsohon sanatan na Kogi ta yamma ya kuma yi alkawarin cewa idan an zabe shi gwamna, zai yi mulki ne tare da 'tsoron Allah'
  • Malaye ya yi nasarar zama dan takarar gwamnan PDP ne bayan yin nasara a zaben fidda gwani da aka yi a ranar 16 ga watan Afrilu

Jihar Kogi - Dino Melaye, dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a zaben ranar 11 ga watan Nuwamba a Kogi, ya ce zai yi gwamnati mai tafiya da kowa-da-kowa idan an zabe shi.

A cikin sanarwar da tawagar watsa labaransa ta fitar a ranar Asabar, dan takarar na PDP ya yi magana ne yayin ziyarar da ya kai fadar Abdulrazak Isa Koto, Ohimege Igu na Koton Karfi.

Kara karanta wannan

Binani ce ta ci zabe: Hudu Ari ya fasa kwai, ya ce manya a INEC sun karbi cin hanci daga Fintiri

Dino Melaye
Dino Melaye ya ce zai yi mulki ba tare da nuna banbancin kabila ba idan an zabe shi gwamnan Kogi. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Ba zan nuna banbancin kabila ba kuma mulki da tsoron Allah zan yi a Kogi - Dino Melaye

Tsohon sanatan mai wakiltar Kogi ta Yamma ya ce zai yi mulkin jihar "da tsoron Allah" idan an zabe shi, The Cable ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Melaye ya kara da cewa zai zama 'gwamna na kowa" ba tare da la'akari da kabila ba.

Dan takarar na PDP ya ce:

"Kamar yadda ka sani, Mai Martaba, cikin shekaru 4 a matsayin sanata, na yi ayyuka 19 a karamar hukumar Kogi. Ina da alaka ta musamman da Kogi da izinin Allah, idan an zabe ni gwamna, zan mayar da hankali kan bukatun mutanenka, musamman kallubale na muhalli a yankin.
"Mun san cewa babban sana'ar mutane a nan ita ce noma da sifiri. Za mu mayar da hankali kan wadannan bangarorin a gwamnatinmu ta hanyar karfafa wa mutanenmu gwiwa.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Kogi: Shugaba Buhari Ya Yarda Ododo Ya Gaji Yahaya Bello

"Zan zama gwamnan Kogi wanda zai yi mulki da tsoron Allah, zan tafi tare da kowa ba wai a matsayin Igala, Ebira, Okun, Kakanda, Bassa, Koto ko Nupe ba amma gwamna na kowa karkashin jagorancin Allah mai girma.
"Na taya ka murna a matsayin shugaban masu sarautun gargajiya na Kogi ta Yamma kuma ina addu'a karkashin jagorancinka, Kogi ta Yamma za ta samar da gwamna, don haka, ina neman albarkanka a yayin da muke tunkarar zabe."

A ranar 16 ga watan Afrilu, Melaye ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan Kogi a PDP, inda ya kada Idoko Ilonah, babban abokin karawarsa da kuri'u 189.

Zai fafata da Ahmed Ododo, na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a zaben gwamnan da aka shirya yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Katafaren gida da Dino Melaye ya gina a matsayin masaukinsa na garinsu

Sanata Dino Melaye ba yana cigaba da rayuwarsa da ya saba na nuna wa duniya falalar da ubangiji ya masa na samun yalwa da rayuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Tsaida Ranakun Bude Titunan Kano-Zaria-Kaduna, Legas-Ibadan, da Gadar Neja

A wani bidiyo da ya fitar, Melaye ya nuna wa duniya wani katafaren gida da ya gina a kauyensu na Aiyetoro, Gbede, jihar Kogi a matsayin masaukinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel