Bidiyon 'aljannar duniya' da Dino Melaye ya gina a matsayin masaukinsa na kauye

Bidiyon 'aljannar duniya' da Dino Melaye ya gina a matsayin masaukinsa na kauye

Fitaccen dan siyasan Najeriya, Sanata Din Melaye, ya cigaba da rayuwarsa mai cike da facaka da waddaka da dukiya kuma ya na wallafa motoci, gidaje da sauran kayan alatu a kafafe sada zumunta.

A sabuwar wallafar da ya yi a shafinsa na Facebook, tsohon sanata mai wakiltar Kogi ta yamma, ya wallafa bidiyon gidansa na kauyensu da ke Aiyetoro, Gbede a jihar Kogi.

Bidiyon 'aljannar duniya' da Dino Melaye ya gina a matsayin masaukinsa na kauye
Bidiyon 'aljannar duniya' da Dino Melaye ya gina a matsayin masaukinsa na kauye. Hoto daga Dino Melaye
Asali: Facebook

A wani bidiyo da Legit.ng ta gani, wata murya wacce ba a san ko ta waye ba ta nuna sashi daban-daban na gidan wanda ya bayyana katafare.

"Wannan ne farfajiyar gidan Sanata Melaye a kauyensu na Aiyetoro da ke Gbede a karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi," muryar ta sanar a wani bidiyo yayin da aka fara zagaye gidan.

Kara karanta wannan

Dattawan Zamfara sun zargi hukumomin tsaro da sakin 'yan bindigan da suka kama

Dankarerren bene da dakin maza

Wanda ke bayar da labarin ya nuna sassan gidan inda aka ga bene mai launin fari da kuma dakin maza mai dakunan kwana shida.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bene ne, katafaren gida kuma ya na da fili sosai," mai maganar ya cigaba da cewa yayin da ya ke nuna sassan ginin.
"Akwai wani fili da ke tsakanin asalin cikin gidan da kuma dakin yara maza," ya kara da cewa.

Kamar yadda mai maganar ke fadi, dakin yara mazan kawai ya kunshi dakunan kwana shida.

"Kuna ganin gidan, katafaren gida ne mai kunshe da farfajiya mai girma," mai bayar da labarin ke fadi yayin da ya ke nuna cikin gidan.

Sashin wasanni da kuma cocin da Melaye ke bauta

A baya dakunan yara maza ne akwai babban fili inda akwai wurin wanka, wurin wasan Tennis da Volley Ball.

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar Korona: An hana wuraren ibada da gidajen shakatawa a Abuja taro

Duk a wannan filin akwai katafaren coci, wanda kamar yadda mai bada labarin ke fadi, jigon jam'iyyar PDP ya gina domin lada ta kai ga mahaifiyarsa.

Sanata Melaye na bauta a cocin a duk lokacin da ya je kauyen, in ji mai bayar da labarin.

Wanne martani 'yan Najeriya suka yi?

A yayin tsokaci kan bidiyon da aka wallafa a Facebook, Ehinmole Oluwatomisin Lawumi Justsu ya ce:

"A gaskiya wannan abun ya yi kyau, ganin wannan katafaren gidan da ka mallaka a kauyen ku ya kara maka kima a ido na, Ubangiji ya karo maka albarka."

Aderemi Adeeko ya ce:

"Farfajiya babba kuma mai kyau tare da sassa masu yawa."

Kenny Momoh yace:

"SDM, bayan na kalla wannan bidiyon duk da na san wurin nan sosai, me ye amfanin wannan bidiyon? Ina fatan za ka kammala gidan man ka da wurin saide-saide da ke Aiyetoro Gbede domin amfanin kowa."

Kara karanta wannan

Coca Cola ta kaddamar da 'Project EQUIP' a Kano: Ga Muhimman abubuwa 3 da shirin zai mayar da hankali a kai

Hotuna da bidiyon motar N460 miliyan da Dino Melaye ya siya

A wani labari na daban, Dino Melaye, tsohon sanata da ya taba wakiltar yankin Kogi na yamma, ya darzo sabuwar motar kirar Lamborghini Aventador Roadstar.

Tunde Ednut ne ya wallafa hotuna tare da bidiyon motar alfarmar a shafinsa a ranar Asabar da ta gabata.

Fitaccen sananne a shafukan sada zumuntar ya wallafa hoton tsohon dan majalisar yana tuka motarsa mai darajar dala miliyan daya wanda yayi daidai da N460,000,000.

"Sanata Dino Melaye ya siya sabuwar mota kirar Lamborghini Aventandor Roadstar kirar 2020. Kamfanin sun fitar da ita ne a bikin cikarsu shekaru 50. Wannan tana daya daga cikin guda 100 da kamfanin suka yi su a kan dala miliyan 1," ya wallafa a Instagram.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel