Rivers: Gwamna Ya Kuma Ɗaga Yatsa Ga Wike, Ya Bugi Kirji Kan Jikkata Abokan Gaba

Rivers: Gwamna Ya Kuma Ɗaga Yatsa Ga Wike, Ya Bugi Kirji Kan Jikkata Abokan Gaba

  • Yayin da rikicin jihar Rivers ke kara kamari, Gwamna Siminalayi Fubara ya bayyana nasarar da ya samu kan makiya
  • Simi Fubara ya ce ya yi nasarar murƙushe abokan gaba da suke neman kawo masa cikas a cikin gwamnatinsa a jihar
  • Gwamna ya ce madadin su ga gazawar gwamnatinsa a yayin bikin cika shekara daya, sune suke kwana da idanu a bude

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya bugi kirji kan yadda ya yi nasara kan makiya a jihar.

Simi Fubara ya ce ya murƙushe dukkan abokan gaba da suke neman kawo cikas a ci gaban jihar Ribas da yake mulka.

Kara karanta wannan

"Ko a jikina," Ministan Tinubu ya maida martani kan abubuwan da ke faruwa a Rivers

Gwamna ya sake taɓo Wike kan siyasar Rivers
Gwamna Siminalayi Fubara ya sake taɓo Nyesom Wike inda ya ce ya yi nasara kan abokan gaba. Hoto: Siminalayi Fubara, Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Rivers: Fubara ya yi shaguɓe ga Wike

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya ke jawabi ga Kungiyar matasa ta Ijaw Youth Council (IYC) a jiya Alhamis 16 ga watan Mayu, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne yayin da rikicin siyasar jihar ke kara ƙamari tsakanin Gwamna Fubara da tsohon mai gidansa, Nyesom Wike.

Hakan ya jawo sake murabus din karin akalla kwamishinoni hudu a gwamnatin Fubara a wannan mako.

Sai dai duk da haka, Fubara ya ce ya yi nasarar dakile makiyan jihar Rivers da suke ganin sai da su za ta ci gaba, Punch ta tattaro.

Fubara ya bugi kirji a Rivers

"Da ikon ubangiji, abin da suke tunanin za su mana yayin murnan cika shekara daya a ofis, sune suke kwana da ido a bude."

Kara karanta wannan

Kwamishina na 4 ya yi murabus daga muƙaminsa, ya tura wasiƙa ga Gwamna Fubara

"Wannan shi ya tabbatar muna da jinin Ijaw a jikinmu, watau jinin aiki ba yawan surutu ba da kame-kame."

- Siminalayi Fubara

Fubara ya sha alwashin ci gaba da kawo ayyukan ci gaba a jihar saboda makiya su sake ta da hankalinsu.

Wike ya ba da hakuri kan Fubara

A wani labarin, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ba da hakuri kan kuskuren da ya tafka a jihar Rivers.

Wike ya ce ya yi nadamar zaben Gwamna Siminalayi Fubara a matsayin magajinsa da ya daura kujerar gwamna.

Tsohon gwamnan ya sha alwashin gyara kura-kurai da ya aikata kan matakin inda ya ce zai gyara su a zabe mai zuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel