Shugaba Buhari Ya Caccaki Gwamna Ortom, Ya Faɗi Abinda Ya Janyo Masa Rashin Nasara

Shugaba Buhari Ya Caccaki Gwamna Ortom, Ya Faɗi Abinda Ya Janyo Masa Rashin Nasara

  • Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi wa gwamnan Ortom na Benuwai shaguɓe kan rashin nasarar cika burin zama Sanata
  • A wata sanarwa da Mallam Garba Shehu ya fitar ranar Laraba, Buhari ya ce mutanen Benuwai sun yanke hukuncin da ya dace
  • Samuel Ortom, mamban PDP, ya sha ƙasa a yunkurinsa na tafiya majalisar dattawa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023

Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ranar Talata 18 ga watan Afrilu, 2023 ya waiwayi gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, kan gaza kai labari a burinsa na zama Sanata a 2023.

Shugaba Buhari ya yi wa gwamna Ortom na jam'iyyar PDP shaguɓe bisa kashin da ya sha a zaɓen Sanatoci ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Buhari da Ortom
Shugaba Buhari Ya Caccaki Gwamna Ortom, Ya Faɗi Abinda Ya Janyo Masa Rashin Nasara Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Buhari ya yi ikirarin cewa talakawan jihar Benuwai sun yi watsi da burin Ortom na tafiya majalisar dattawa saboda suna zargin bai tabuƙa komai ba tsawon shekaru Takwas.

Kara karanta wannan

Ziyarar Umrah: Buhari ya dawo Najeriya bayan shaefe kwanaki 8 a kasar Saudiyya

Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Mun gode Allah, mutanen jihar Benuwai sun guje shi ranar zaɓe, sun ƙi sabunta kwantiraginsa, ya sha kaye a zaben Sanata, har wanda ya tsayar takarar gwamna bai kai labari ba."
"Sun fi kowa sanin halin da mutane ke rayuwa a jihar Benuwai, duk wanda yake laluben wanda ke da laifi ya tambayi mazauna jihar Benuwai."

Meyasa Ortom ya sha kaye?

Shugaban ƙasan ya zargi gwamna mai barin gado da gurgunta duk wani yunkurin gwamnatin tarayya na magance matsalar tsaro a jihar Benuwai.

Buhari ya ƙara da cewa maimakon gwamna Ortom ya rungumi namijin ƙoƙarin da gwamnati take yi, amma shi gwamna ya maida hankali ne wajen sanya siyasa a kan komai.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wannan maganganu ne a wata sanarwa da babban kakakinsa, Mallam Garba Shehu, ya fitar ranar Laraba, 2023, kamar yadda Channels ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Tona Asirin Gidansa, Ya Fallasa Yadda Iyalansa Suka Zaɓi Peter Obi a 2023

Ya ƙara da cewa mutanen jihar Benuwai sun samu natsuwa da kwanciyar hankali a ransu saboda gwamna Ortom na dab da sauka daga mulki yayin da sabon gwamna mai adalci zai hau.

Gwamna Fintiri Ya Karbi Shaidar Lashe Zaben Gwamna

A wani labarin kuma INEC Ta Baiwa Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Adamawa Shaidar Samun Nasara

Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa a abokiyar takararsa, Farfesa Farauta sun karbi shaidar cin zaɓe daga hannun hukumar zaɓe.

Wannan na zuwa ne awanni 24 bayan baturen zaɓe ya ayyana Fintiri a matsayin wanda ya ci zaben gwamnan da aka ƙarisa ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel