Ku Mara Mun Baya Na Dawo Da Sokoto Kan Turba, Zababben Gwamna Ga PDP

Ku Mara Mun Baya Na Dawo Da Sokoto Kan Turba, Zababben Gwamna Ga PDP

  • Gwamnan Sakkwato mai jiran gado, Ahmed Aliyu, ya karbi shaidar lashe zabe daga hukumar INEC ranar Alhamis
  • Da yake jawabi, Ahmed Aliyu ya roki jam'iyyun siyasa su ba shi haɗin kai wajen ci da jihar zuwa gaba
  • Jam'iyyar APC ta lallasa PDP mai mulki a zaɓen gwamnan da ya gudana ranar 18 ga watan Maris, 2023

Sokoto - Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya ce yana da bukatar goyon bayan jam'iyar PDP da sauran jam'iyyun siyasa a kudirinsa na dawo jihar kan turba.

Daily Trust tace Aliyu ya faɗi haka ne ranar Alhamis bayan shi da mataimakinsa mai jiran gado, Idris Mohammed Gobir, sun karɓi shaidar cin zaɓe daga INEC.

Zabbaben gwamnan Sakkwato.
Lokacin da zababben gwamna, Ahmed Aliyu, ya karbi shaidar cin zabe Hoto: Ahmed Aliyu
Asali: Facebook

Baki ɗaya zababbun mambobi 30 na majalisar dokokin jihar sun karbi Satifiket ɗin shaidar cin zabe a wurin kwaryakwaryar bikin da aka shirya a zauren tattara sakamakon INEC da ke gefen titin Tangaza.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito: 'Yadda Aka Mun Tayin Makudan Kuɗi da Barazanar Kisa Na Canja Sakamakon Zaben Gwamna'

Jam'iyyar APC ta lashe kujerun yan majalisar jihar guda 20 yayin da babban abokiyar karawarta PDP ta samu kujeru 10.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin gwamna mai jiran gado

A jawabinsa bayan ya karbi shaidar zama zaɓaɓɓen gwamna, Aliyu ya nemi goyon bayan jam'iyyun adawa domin dawo da jihar Sakkwato kan turba mai kyau.

"Wannan nasarar ba tawa bace ni kaɗai, nasara ce ta kowane mazaunin jihar Sakkwato, wadanda su ka zaɓi canji. Saboda haka ina roƙon mambobin jam'iyyun adawa su haɗa hannu da ni mu ɗaga darajar jiharmu."

"Mu haɗu wuri ɗaya mu dawo da jihar mu kan turbar da aka santa domin kowa ya amfana," inji Ahmed Aliyu.

Tun da farko, kwamishinan hukumar INEC mai kula da jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara (REC), Farfesa Muhammad Sani Kalla, ya ce zaɓe ya zo kuma ya wuce, mutane sun zaɓi wanda suke so.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: Babban Abinda Ya Sa Abba Gida-Gida Ya Lallasa APC a Zaben Gwamna a Kano

A cewarsa, gudummuwar da kowane mai ruwa da tsaki ya bayar abun a yaba ne. Ya roki Allah ya dafa wa zababbun shugabanni su bi hanya madaidaiciya.

Ina da Ikon Naɗa Kowa Na So Har Zuwa Ranar 29 Ga Watan Mayu, Ortom

A wani labarin kuma Gwamnan Benuwai ya maida martani ga masu sukar naɗe-naɗen da yake yi yayin da mulkinsa ya kusa karewa

Ortom, mamban jam'iyyar PDP, ya ce har zuwa ranar 29 ga watan Mayu, yana da ikon naɗa duk wanda ransa yake so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel