Yadda Aka Matsamun Lamba da Makudan Kuɗi na Canja Sakamakon Zaben Gwamna, VC

Yadda Aka Matsamun Lamba da Makudan Kuɗi na Canja Sakamakon Zaben Gwamna, VC

  • Shugabar jami'ar FUTO, Farfesa Nnenna Oti, ta ce ta fuskanci abubuwa daban-daban don canja sakamakon zaben gwamna a Abiya
  • Oti, baturiyar zabe a Abiya, ta ce an mata tayin makudan kuɗaɗe da barazana da rai amma ta ce ba gudu ba ja da baya
  • INEC ta ayyana dan takarar LP, Alex Otti a matsayin wanda ya zama zaɓaɓɓen gwamnan jihar Abiya bayan kai ruwa rana

Abia - Baturen zaɓe mai alhakin tattara sakamakon zaɓen gwamna a jihar Abiya, Farfesa Nnenna Oti, ta fallasa yadda aka bata cin hancin makudan kuɗi ta canja sakamako.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa yau mako ɗaya kenan da INEC ta ayyana Alex Otti na jam'iyyar Labour Party a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a Abiya.

Nnenna Oti.
Shugaban jami'ar FUTO, Farfesa Nnenna Oti Hoto: dailytrust
Asali: UGC

A sakamakon da ta sanar a Ofishin INEC da ke Abiya, ɗan takarar LP ya samu kuri'u 175,467, wanda ya ba shi damar lallasa babban abokin karawarsa na PDP, Ahiwe, wanda ya samu kuri'u 88,529.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: Babban Abinda Ya Sa Abba Gida-Gida Ya Lallasa APC a Zaben Gwamna a Kano

Farfesa Oti, ta faɗi halin da ta shiga ne yayin da take jawabi lokacin da ma'aikata da ɗaliban jami'ar fasaha ta tarayya da ke Owerri (FUTO) suka fito tarba da mata maraba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugabar jami'ar, Oti, ta ce gabanin ta ayyana sakamakon zaben gwamnan, an mata alƙawarin maƙudan kuɗaɗe masu nishi domin ta canja zaɓin mutanen Abiya.

"A matsayin jami'ar zaɓe, ban taɓa kwatanta aikin zaɓe ba a rayuwata amma kaddara ta kira ni, aka neme daga Abuja. Idan na mutu na mutu kenan, sun yi barazana, sun zo da kuɗi."

VC ta ƙara da cewa duk da haka ba ta karaya ba, ta tsaya kai da fata kan ƙa'idoji da dokoki domin tabbatar da babu wanda ya canza muradin mutanen Abiya.

"Ina tsaye gabanku, Allah na gani ban taba damfarar kowa ba, na bayyana musu ƙa'idoji na cewa, indai ni ce dole kowace kuri'a ta yi aiki. Karkashina, dole a baiwa mutane haƙƙinsu na wanda suka zaɓa."

Kara karanta wannan

Ana Azumi Dandazon Mata Sun Fito Zanga-Zanga a Jihar Kaduna, Sun Faɗi Buƙatarsu

"Saboda ni Farfesa Nnnena Oti, ba zan taɓa aikata sheɗanci ba," inji shugabar jami'ar FUTO.

Babban Abinda Ya Jawo APC Ta Sha Kaye a Kano

A wani labarin kuma Babban jigon APC ya fallasa babban dalilin da yasa Abba Gida-Gida ya ci zaben gwamna a jihar Kano

Tsohon ɗan takarar shugaban matasa, Abba Dangata, ya ce rigingimun cikin gida ne ya kawo ƙarshen mulkin APC a jihar Kano.

Ya ce matukar gwamnatin Kano ba ta canja salon mulki ba, APC ba ta daina ware wasu shafaffu da ma, rashin nasara yanzu ta fara gani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel