Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Ya Rasa Kujerar Sa

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Ya Rasa Kujerar Sa

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Zamfara ta karɓe muhimman kujeru a majalisar dokokin jihar
  • Jam'iyyar PDP ta kayar da wasu daga cikin shugabannin majalisar kuma ƴan takarar jam'iyyar APC a zaɓen na ƴan majalisar dokokin jihar
  • Kakakin majalisar dokokin jihar na daga cikin waɗanda guguwar sauyi tayi awon gaba da su a jihar

Jihar Zamfara- Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Nasiru Muazu Magarya, na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya sha kashi ƙoƙarin sa na sake komawa majalisa.

Nasiru Muazu Magarya ya rasa kujerar sa ne a hannun ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Bilyaminu Ismail, a mazaɓar Zurmi ta Gabas. Rahoton Channels Tv

Zamfara
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Ya Rasa Kujerar Sa Hoto: Channels tv
Asali: UGC

Baturen zaɓen ƙaramar hukumar Zurmi, Mudassir Moriki ya bayyana cewa Magarya ya samu ƙuri'u 9,530, yayin da abokin hamayyar sa na jam'iyyar PDP, Bilyaminu Ismail ya samu ƙuri'u 11,213.

Kara karanta wannan

Bayan Shan Kashi a Zaben Gwamna, Dan Takarar APC Yayi Wani Muhimmin Abu Daya Rak

“Ni Muddasir Ismail, baturen zaɓen mazaɓar Zurmi ta Gabas a zaɓen majalisar dokokin jiha da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris 2023, ƴan takara sun fafata a zaɓen inda suka samu ƙuri'u kamar haka," Inji shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mu’azu Nasiru na APC ya samu ƙuri'u 9,530 sannan Isma’il Bilyaminu na PDP ya samu ƙuri'u 11,213.”

Haka kuma mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Musa Bawa Yankuzo, ya rasa kujerar sa a hannun Bello Maza-Waje na jam'iyyar PDP. Shima mataimakin jagoran majalisar dokokin Nasiru Lawal Bungudu, ya sha kashi a hannun Bashiru Dan-Meri na PDP. Rahoton Punch

Haka nan shi ma shugaban kwamitin ilmi na majalisar dokokin jihar, Alhassan Kanoma, yayi rashin nasara a hannun ɗan takarar jam'iyyar PDP, Nasiru Abdullahi.

Dan Takarar Gwamnan Jihar Oyo Na APC Ya Rungumi Kaddara Ya Taya Abokin Karawar Sa Murna

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Yi Babban Abun Kunya, Jam'iyar PDP Ta Kwace Kujerun Yan Majalisu 25 Cikin 26 a Jiha 1

A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar gwamnan jihar Oyo yayi wani muhimmin abu bayan ya sha kashi a zaɓen gwamnan jihar da aka gudaɓar.

Teslim Folarin na jam'iyyar All Progressives Congress ya kai zuciya nesa inda ya abokin karawar sa kuma gwamna mai ci a yanzu, Seyi Makinde, na jam'iyyar Peoples Democratic Party.

Asali: Legit.ng

Online view pixel