UTME 2024: Gwamnan Kwara Ya Mika Sako Ga Daliban da Suka Ci Mai Yawa a JAMB

UTME 2024: Gwamnan Kwara Ya Mika Sako Ga Daliban da Suka Ci Mai Yawa a JAMB

  • Gwamnan jihar Kwara ya yabawa daliban da suka ci jarrabawar UTME a jiharsa da ma Najeriya baki daya a kwanan nan
  • An saki jarrabawar JAMB, inda ake ci gaba da ganin makin da dalibai suka samu a wannan shekarar da kuma wadanda suka yi nasara
  • Jarrabawar UTME da hukumar JAMB ke shirya itace kofar shiga jami’o’in Najeriya, musamman duba da adadin da ake samu na yawan dalibai

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

ihar Kwara - Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana farin cikin samun rahotannin yadda dalibai suka yi kwazo a jarrabawar shiga jami’a ta UTME da JAMB gudanar kwanan nan.

Kara karanta wannan

An shiga jimamin rashin daliba Aishat a jami'ar Aliko Dangote bayan tsintar gawarta a daki

Gwamnan ya ce babban abin da ya fi daukar hankalinsa shine sakamakon da Samuel Oluwasemilore na Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Omu Aran, inda dalibin ya sami maki 358 a jarabawar.

Gwamna ya yabi daliban da suka ci JAMB
Gwamnan Kwara ya yaba da kwazon 'yan JAMB a bana | Hoto: RealAARahman
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwar da gwamnan ya fitar ta hannun babban sakataren yada labaransa, Rafiu Ajakaye, ya kuma taya dalibai 30 na Eucharistic Heart of Jesus Model College da ke Kwara murnar samun maki 300 zuwa 355 a jarrabawar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanan da gwamnan Kwara ya yi

A cewar sanarwar:

“Muna alfahari da nasarori irin wadannan; suna zama misali ga matasa don yin aiki tukuru, su kasance masu iya kokarinsu a karatunsu, kuma su sanya iyayensu da al'umma alfahari.”

Hakazalika, ya bayyana jin dadinsa da yadda aka samu hazikan dalibai a jiharsa, inda ya kuma yaba da yadda jihar ta wakilci Najeriya kwanan nan a kasar Singapore.

Kara karanta wannan

Borno: Gwamna Zulum ya tafka babban rashi yayin da hadiminsa ya rasu

‘Yan Najeriya dai mutane ne masu kwazo, kuma sukan zama misali ga al’ummar duniya a duk inda suka tsinci kansu.

Jarrabawar UTME ta bana ta sake tabbatar da yadda ake samun dalibai masu tasowa a nan gaba, wadanda za su iya kawo sauyi mai kyau ga kasar nan.

Dalibi ya samu maki 313 a jarrabawar UTME

A bangare guda, bayan samun maki 313 a jarrabawar shiga manyan makarantu (UTME), dan shekaru 18, Ebeniro Akachi, ya tabbatarwa duniya cewa ana yin nasara idan aka yi aiki tukuru.

Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar JAMB ta fitar da sakamakon jarabawar UTME ta shekarar 2024 a ranar Talata, 29 ga watan Afrilu.

Akachi ya yi nasarar samun maki 313 daga darusa hudu da ya amsa tambayoyi a kansu a jarabawar da ya zana a karo na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.