Muhimman Abubuwa 10 Game Da Nasiru Yusuf Gawuna Dan Takarar Gwamnan Kano Na APC

Muhimman Abubuwa 10 Game Da Nasiru Yusuf Gawuna Dan Takarar Gwamnan Kano Na APC

A ranar Asabar 18 ga watan Maris yan Najeriya za su fita su jefa wa yan takarar gwamna da suke ra'ayi kuri'unsu.

Gabanin wannan babban ranar, akwai wasu yan takarar gwamna wadanda yan jam'iyyun hamayya sai sun yi da gaske za su iya nasara a kansu.

Nasiru Gawuna
Wasu bayanai game da Nasiru Gawuna, dan takarar gwamnan Kano a APC. Hoto: Photo credit: @AbubakarmusaDK1
Asali: Twitter

Muhimman abubuwa game da Gawuna da ka iya daukan hankalin yan Najeriya gabanin zaben

Masu kada kuri'a wadanda suka gamsu da ayyukan yan siyasan da ke takarar kujeru daban-daban don yi wa mutanensu aiki ne za su yanke hukuncin karshe kan yan takarar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ba tare da dogon jawabi ba, Legit.ng ya haska kan wasu abubuwa masu muhimmanci da jan hankali game da dan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar APC wanda shine zabin Abdullahi Ganduje a matsayin magajinsa.

Dr Nasiru Gawuma
Wasu abubuwa 10 masu ban sha'awa game da Gawuna, dan takarar gwamnan Kano na APC. Hoto: Photo credit: @AbubakarmusaDK1
Asali: Twitter

1. Nasiru Gawuna ma'aikacin lafiya ne a Najeriya, dan kasuwa kuma dan siyasa

2. A watan Mayun 2022, ya zama dan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress, APC na babban zaben 2023

3. Gawuna ya taba rika mukamin ciyaman na karamar hukuma sau biyu, shugaban ALGON sau biyu, kuma amintaccen kwamishina ne na karamar hukuma.

4. Ya kama aiki a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kano a ranar 19 ga watan Satumban 2018, Dr Nasir Gawuna ya zama mataimakin gwamna bayan murabus din tsohon mataimakin gwamna Farfesa Hafiz Abubakar a 2018.

5. Gawuna ne tsohon kwamishinan noma na jihar Kano.

6. Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ne ya fara nada shi a matsayin kwamishina.

7. Gawuna ne ciyaman din tawagar yaki da cutar COVID-19 na jihar Kano.

8. Shine shugaban karamar hukumar Nasarrawa a jihar Kano na tsawon shekaru takwas karkashin rushashiyar jam'iyyar All Nigeria's Peoples Party, ANPP, yayin da Ibrahim Shekarau ke gwamnan jihar Kano; hakan na nufin ya yi aiki da gwamnoni uku a jihar.

9. A halin yanzu shine mataimakin gwamnan jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

10. Fitaccen dan siyasan ya fice daga ANPP, jam'iyyar da ya shiga tun 1999 zuwa 2014; kuma ya shiga jam'iyyar APC mai mulki a shekarar ta 2014.

Takaitawa

Dr Nasir Yusuf Gawuna ya zama mataimakin gwamna bayan murabus din tsohon mataimakin gwamna Farfesa Hafiz Abubakar a 2018

Gawuna ne kwamishinan ayyukan noma kafin ya zama mataimakin gwamna. Kuma shi kwamishina ne yayin gwamnatin Gwamna Kwankwaso kuma shine shugaban karamar hukumar Nasarrawa lokacin mulkin Malam Ibrahim Shekarau.

Kazalika, yana takara a yanzu a shekarar 2023 don neman gaje gwamnan Kano mai ci a yanzu, Ganduje.

Gwamnan Katsina Masari ya tattauna da Buhari game da zaben gwamna da ke tafe

Aminu Bello Masari, gwamnan jihar Katsina ya ce yana sa ran Dikko Radda, dan takarar gwamna na jihar Katsina zai yi nasara a zaben da ke tafe.

Gwamnan Katsinan ya furta hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a ranar Laraba yayin da ya kai wa Shugaba Buhari ziyara a gidansa da ke Daura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel