Ganduje: Mai Neman Kujerar APC Ya Sake Bankaɗo Matsala Kan Shugaban Jam'iyya

Ganduje: Mai Neman Kujerar APC Ya Sake Bankaɗo Matsala Kan Shugaban Jam'iyya

  • Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan kujerar Abdullahi Ganduje, tsohon mai neman kujerar ya maka shi a kotu
  • Mohammed Sa'idu-Etsu ya bukaci a ayyana kujerar Ganduje a matsayin wacce ba ta halatta ba ganin tsarin da aka bi wurin nada shi
  • Etsu ya shigar da korafin ne a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke birnin Abuja kan sahihancin shugabancin Ganduje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Tsohon mai neman kujerar shugaban APC, Mohammed Saidu-Etsu ya sake shigar da kara kan Abdullahi Ganduje.

Sa'idu-Etsu ya bukaci soke nadin da kwamitin gudanarwa na jami'iyyar ya yi wa Ganduje a matsayin shugaban APC.

Dan takarar shugabancin APC ya maka Ganduje a kotu
Abokin hamayyar Abdullahi Ganduje ya maka shi a kotu kan shugabancin APC. Hoto: Dr. Abdullahi Ganduje.
Asali: Twitter

Wasu korafe-korafe aka shigar kan Ganduje?

Kara karanta wannan

"Buhari ya daura shugaban APC duk da zargin cin N15bn", Tsohon Minista ya tona asiri

A cikin korafi da ya shigar Babbar Kotun Tarayya a Abuja, Etsu ya bukaci ayyana nadin Ganduje wanda bai halatta ba kuma ya saba dokar kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bukaci kotun ta dakatar da shi kan ci gaba da kiran kansa a matsayin shugaban jam'iyyar a nan gaba, cewar Daily Nigerian.

Har ila yau, Etsu ya kalubalanci nadin Ganduje inda ya ce ya kamata a bi tsarin zabe ne a babban taron jam'iyyar a matakin kasa, Sahara Reporters ta tattaro.

Lauyoyi sun bukaci bahasi kan shugabancin Ganduje

Lauyoyin wanda ya shigar da karar, J. Obono-Obla da M.M. Aggrey sun bukaci bahasi kan ingancin Ganduje daga Arewa maso Yamma a matsayin shugaban APC.

Sun bukaci duba kan kundin tsarin jami'iyyar APC na shekarar 2013 wanda aka yi wa gyaran fuska.

Kara karanta wannan

Tinubu yana amfani da Wike wajen ruguza jam'iyyar PDP? Dele Momodu ya magantu

A cikin takardar korafin mai lamba CS/2258/24 ana tuhumar Abdullahi Ganduje da jam'iyyar APC da kwamitin gudanarwa da kuma tsare-tsare.

Mai korafin har ila yau ya ce bai kamata ba bayan murabus din tsohon shugaban APC, Abdullahi Adamu a ba Ganduje dama wanda ya fito daga Arewa maso Yamma.

Kotu ta dakatar da kama 'yan APC

A wani labarin, wata kotu da ke zamanta a Kano ta yi hukunci kan dambarwar da ake yi game da kujerar Abdullahi Ganduje.

Kotu ta dakatar da jami'an 'yan sanda kan kokarin cafke tsagin jam'iyyar APC da suka dakatar da Abdullahi Ganduje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel