“Ba Za a Rasa Kowani Bayani Da Ke Kan BVAS Ba”: INEC Ta Tabbatarwa Kotu Da Peter Obi

“Ba Za a Rasa Kowani Bayani Da Ke Kan BVAS Ba”: INEC Ta Tabbatarwa Kotu Da Peter Obi

  • An baiwa kotun zaben shugaban kasa na 2023 da jam'iyyun siyasa tabbacin cewa babu abun da zai samu bayanan da ke kan na'urorin BVAS
  • Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ita ce ta baiwa Peter Obi na Labour Party da kotun zabe tabbacin
  • A cewar hukumar, za a tura bayanan da ke kan BVAS zuwa kwamfutar hukumar yayin sake saita na'urorin

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa dukkan bayanan da ke kan na'urorin BVAS da aka yi amfani da su a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu na nan daidai.

Tanimu Inuwa, jagoran lauyoyin hukumar a kan lamarin kotun zaben shugaban kasa tsakanin dan takarar Labour Party, INEC da zababben shugaban kasar ne ya bayar da tabbacin a ranar Talata, 7 ga watan Maris a kotun daukaka kara da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: PDP Ta Koka, Ta Ce INEC Na Kokarin Goge Hujja Da Ake Da Shi Kan Nasarar Tinubu

Na'urar hukumar zabe da shugaban INEC, Mahmood Yakubu
“Ba Za a Rasa Kowani Bayani Da Ke Kan BVAS Ba”: INEC Ta Tabbatarwa Kotu Da Peter Obi Hoto: Vanguard, Guardian
Asali: Facebook

Yayin da yake adawa da karar da dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi ya shigar kan BVAS a zaben shugaban kasar, Inuwa ya ce babu abun da zai samu duk bayanan da ke na'urar, rahoton Punch.

Da na'urorin BVAS din za a yi zaben gwamnoni da yan majalisun jihohi

Sai dai kuma, ya sanar da kotu cewa akwai bukatar sake saita na'urorin BVAS domin amfani da su a zaben gwamna da na majalisun jihohi da za a yi a ranar Asabar, 11 ga watan Maris.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Inuwa ya bayyana cewa rashin sake saita na'urorin BVAS zai kawo tsaiko wajen gudanar da zabukan gwamnoni da na yan majalisun jihohi.

Muhawarar lauyan INEC ya biyo bayan gabatar da karar da lauyan Peter Obi, Onyechi Ikpeazu ya yi cewa dalilin bukatar shine don ba tawagar lauyoyin damar kwashe bayan da ke kunshe a na'urorin na BVAS ne.

Kara karanta wannan

Hotuna Sun Bayyana Yayin da INEC Ta Gabatarwa Zababbun Sanatoci Da Satifiket Din Cin Zabe

Ikpeazu ya ce bayanan kan BVAS sune ke wakiltan ainahin sakamakon zaben shugaban kasar wanda aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Ya ce:

"Ya mai girma mai shari'a, wannan don tabbatar da cewar an killace hujjar ne kafin INEC ta sake saita na'urorin na BVAS ne. Hakan ya kasance ne saboda idan aka goge su, zai shafi tasirin shari'ar ne."

Kan haka, Inuwa ya bukaci kotu da ta ki amsa bukatar yana mai cewa amsar bukatar zai shafi shirye-shiryensu kan zabukan gwamnoni da na majalisun jihohi.

Ya kuma sanar da kotun cewa akwai kimanin na'urorin BVAS 176,000 da aka tura rumfunan zabe a yayin zaben shugaban kasar kuma su din ne za a yi amfani da su a zabukan Maris.

Inuwa ya ce:

"Mun rigada mun bayyana a rantsuwarmu cewa babu wani bayani a BVAS da zai bata, za mu tura dukka bayanan na BVAS zuwa na'urarmu.
"Muna bukatar sake saita BVAS din. Don haka, amincewa da wannan bukatar zai shafi tsarin kuma yana iya kawo jinkiri a gudanarwar zabukan."

Kara karanta wannan

Kaico: Tinubu ya yiwa Atiku wankin babban bargo kan zanga-zangar adawa da sakamakon zabe

Bayan ya saurari bangarorin, alkalin da ke jagorantar lamarin Justis Joseph Ikyegh ya dage shari'ar zuwa ranar Laraba, 8 ga watan Maris, rahoton The Cable.

Zan iya shiga tawagar lauyoyin Tinubu bayan 29 ga watan Mayu, ministan Buhari

A wani labarin kuma, Festus Keyamo ya bayyana cewa ba a ga sunansa cikin lauyoyin da ke kare Bola Tinubu bane saboda kasancewarsa minista mai ci, cewa kundin tsari bata bashi dama ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel