"Mun ba ku Mako 2," NLC ta Ja Kunnen Jihohi kan Biyan N30,000 a Mafi Karancin Albashi

"Mun ba ku Mako 2," NLC ta Ja Kunnen Jihohi kan Biyan N30,000 a Mafi Karancin Albashi

  • Kungiyar kwadago ta NLC ta bayyana kaduwa kan yadda har yanzu gwamnonin wasu jihohin kasar nan su ka gaza biyan ma'aikatansu mafi karancin albashin N30,000
  • Shugaban kungiyar, Joe Ajaero yayin tattaunawa da 'yan kungiyar ranar Litinin ya ce abin ya isa haka, tilas ne yanzu gwamnatocin jihohi su fara biyan ma'aikata N30,000
  • NLC ta ba gwamnonin mako biyu su aiwatar da hakan ko kuma su dauki matakin gagarumin yajin aikin gama garin da zai girgiza kowa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Yayin da kungiyoyin kwadago a Najeriya ke fafutukar tabbatar da gwamnati ta biya ma'aikata mafi karancin albashi N615,000, har yanzu akwai jihohin da su ka gaza biyan N30,000.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta sayawa 'yan majalisa motocin alfarma kan N2.6bn

Kungiyar kwadago ta NLC da ta ‘yan kasuwa ta TUC sun gargadi gwamnonin jihohi da su tabbata sun fara biyan N30,000 a karshen watan Mayun da mu ke ciki ko dauki mataki na gaba.

kungiyar kwadago
NLC ta bawa jihohi wa'adin mako 2 Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Punch News ta wallafa cewa kungiyoyin kwadagon sun umarci rassansu da ke jihohi su gaggauta mika wa’adin mako biyu ga gwamnatocinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Za mu dauki mataki,’ NLC

A yau Talata ne kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa kan batun mafi karancin albashi zai ci gaba da zama a teburin tattaunawa domin cimma matsaya.

Ana shirin wannan zama ne kuma kungiyoyin suka umarci ‘ya’yansu da shirin tsunduma yajin aiki matukar gwamnatocin jihohi ba su fara aiwatar da mafi karancin albashin N30, 000 ba.

'Yan NLC sun yiwa gwamnoni barazana

The Guardian ta wallafa cewa NLC ta kara da barazanar rufe kasar nan matukar gwamnatin tarayya ta gaza samar da mafi karancin albashi kafin 13 ga Mayu, 2024.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi:'Ka da gwamnati ta kuskura ta mana tayin N100,000,' TUC

Kungiyar ta kafe a kan ba za ta amince da wani tayi da ya yi kasa da N615,000 ba.

NLC, Gwamnati za su sake zama

A baya mun ba ku labarin cewa kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa domin duba kan mafi karancin albashi da kungiyoyin kwadago za su sake zama ranar Talata domin samun mafiita.

Wakilan kungiyoyin dai sun fice daga dakin taron da kwamitin da Bukar Goni ke jagoranta bayan an yi masu tayin N48,000 a wata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel