"Lashe Zaɓen Tinubu, Nasara Ce Daga Allah, Ku Ƴarda Da Ita", Aisha Buhari Ga Ƴan Najeriya

"Lashe Zaɓen Tinubu, Nasara Ce Daga Allah, Ku Ƴarda Da Ita", Aisha Buhari Ga Ƴan Najeriya

  • Uwargidan shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta nemi ƴan Najeriya da su rungumi nasarar Bola Tinubu, hannu bibbiyu
  • Aisha Buhari ta bayar da tabbacin cewa ɗan takarar ba zai ci amanar da ƴan Najeriya suka ɗora masa ba
  • Uwargidan shugaban ƙasar ta kuma yi wani muhimmin kira kan matar zaɓaɓɓen shugaban ƙasar

Abuja- Uwargidan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta buƙaci ƴan Najeriya da su kawar da son zuciya da bambance-bambance gefe guda su yarda da nasarar Bola Tinubu, a matsayin ƙaddarar ubangiji. Rahoton The Cable

Premium Times ta rahoto cewa Aisha ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis lokacin da ta karɓi baƙuncin Oluremi Tinubu da Nana Shettima, matan zaɓaɓɓun shugaban ƙasa da mataimakin sa a fadar shugaban ƙasa, Abuja.

Aisha Buhari
"Lashe Zaɓen Tinubu, Nasara Ce Daga Allah, Ku Ƴarda Da Ita", Aisha Buhari Ga Ƴan Najeriya Hoto: Thisday Live
Asali: UGC

Ta bayyana cewa nasarar Tinubu nasara ce ga ƴan Najeriya, inda ta bayar da tabbacin cewa ba zai yaudari ƴan Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari Tayi Magana Kan Nasarar Tinubu, Ta Ba Ƴan Najeriya Wani Muhimmin Tabbaci

“Ba tare da la'akari da son zuciyar mu da bambance-bambance ba, yakamata mu duka mu yarda da nasarar shi a matsayin ƙaddarar ubangiji, ba zamu iya ba sai da ikon sa." A cewar Aisha

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Nasara ce ga dukkanin ƴan Najeriya. Ina da fatan cewa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ba zai ci amanar yarda da amincin da ƴan Najeriya suka ɗora masa ba".
"Yanzu lokaci yayi da yakamata mu mayar da hankali kan ciyar da mata da matasa kan gaba."
“Saboda haka, ƴar'uwa ta muna fata kan ƙwarewar ki da gogewar ki wajen ganin kin ciyar da muradun mata, matasa da karatun ilmin ƙananan yara mata, gaba"

Ta kuma ƙarfafa guiwar uwargidan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da ta cigaba da taimakawa mata da ƙananan yara da sana'o'i a ƙasar nan.

2023: Babu Sauran Gardama Tinubu Ne Zabin Ƴan Najeriya, Adamu

Kara karanta wannan

Firaministan Ingila Yayi Magana Kan Nasarar Tinubu, Yayi Masa Wani Muhimmin Alƙawari

A wani labarin na daban kuma, shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, yace ƴan Najeriya sun tabbatar da cewa Bola Tinubu shine zaɓin su.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, shine wanda hukumar zaɓe ta INEC ta bayyana a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng