Atiku Ya Kunyata a Gida, Peter Obi Ya Dankara PDP da Kasa a Kauyen Jihar Adamawa

Atiku Ya Kunyata a Gida, Peter Obi Ya Dankara PDP da Kasa a Kauyen Jihar Adamawa

  • Mazabar Muchalla da ke karkashin karamar hukumar Mubi ta Arewa ta fada hannun Peter Obi
  • Tsayawa takarar Atiku Abubakar, mutumin jihar Adamawa bai hana Jam’iyyar LP ta doke PDP ba
  • A zaben 2019, Peter Obi ya tsaya takara ne tare da Wazirin Adamawa a karkashin jam’iyyar PDP

Adamawa - Jam’iyyar hamayya ta Labour Party ta samu gagarumar nasara a kan jam’iyyar PDP a mazabar Muchalla a karamar hukumar Mubi ta Arewa.

Daily Trust ta rahoto cewa Peter Obi ne ya yi nasara a wannan mazaba da ke jihar Adamawa, duk da cewa Atiku Abubakar yana takara a jam’iyyar PDP.

Abin da zai kara ba mutane mamaki da zaben nan shi ne ana ganin ‘dan takaran na PDP yana da karfi a yankin Arewa maso gabas, musamman mahaifarsa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Dino Melaye Ya Kawo Wa Atiku Akwatinsa A Kogi, Duba Sakamakon

Rahoton ya ce baya ga shi mutumin jihar Adamawa ne, Wazirin Adamawa yana da ta-cewa a yankin, kuma PDP take rike da gwamnatin jiha tun 2019.

Sakamakon zaben da hukumar INEC ta fitar a karamar hukumar Mubi ta Arewa, ya tabbatar da cewa Peter Obi ya tashi da kuri’a 4524 a jam’iyyar LP.

Shi kuma Atiku Abubakar ya samu kuri’u 1, 864 ne a jam’iyyar PDP. Wanda ya zo na uku shi ne ‘dan takaran jam’iyya mai-ci, Bola Tinubu da kuri’u 340.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atiku
Atiku Abubakar a rumfar zabe Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Kuri’u 31 suka tafi ga Rabiu Kwankwaso na New Nigerian Peoples Party (NNPP) a kaf Muchalla.

Ga dai yadda sakamakon zaben nan ya kasancw:

APC 340

LP 4524

NNPP 31

PDP 1864

Adadin masu rajista 16350

Adadin wadanda aka tantance 7020

Adadin kuri’un da aka kada 6995

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Tashi da Kuri’a 1 Kacal Yayin da Atiku Ya Kawowa PDP Akwatinsa

Adadin kuri’un da aka karba 6826

Adadin kuri’un da aka soke 169

LP ta karbe Aso Rock

A wani rahoto da aka fitar kafin yanzu, kun samu labari manyan Jam’iyyun siyasa na APC da PDP sun sha kasa a duka rumfunar zabe da ke fadar Aso Villa.

Baya ga haka a wuraren da ake tunanin APC za ta samu gagarumar nasara a Legas, Peter Obi ya tsinci kuri’u, yayin da Atiku Abubakar yake zuwa na uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel