Yadda Na Tsira Daga Mummunan Harin Kisan Kai, Kakakin Majalisar Osun

Yadda Na Tsira Daga Mummunan Harin Kisan Kai, Kakakin Majalisar Osun

  • Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton yan daban siyasa ne sun farmaki kakakin majalisar dokokin jihar Osun
  • Timothy Owoeye, ya ce yana cikin ganawa da wata ƙungiya a ofishinsa dake Ilesa ba zato maharan suka bude masu wuta
  • Jam'iyyar APC da PDP sun fara musayar yawo kan zargin kashe mambobinsu a jihar Osun

Osun - Kakakin majalisar dokokin jihar Osun, Timothy Owoeye, ya bayyana yadda ya tsira daga harin yan daban siyasa da suka yi yunkurin kashe shi a Ilesa da ke mazabar Sanatan Osun ta gabas.

Wannan harin na zuwa ne yayin da manyan jam'iyyu All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) ke musayar yawu suna zargin juna da kisan mambobinsu a garin.

Timothy Owoeye.
Kakakin Majalisar Osun, Timothy Owoeye. Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Da yake jawabi ga manema labarai, Mista Owoeye, ya ce jami'an tsaron da ke tare da ayarinsa ne suka yi kokarin dakile yunƙurin maharan, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Takarar Sanata da Wasu Mutane 5 Saura Kwana 3 Zaɓe

A cewarsa, 'yan daban da ake zaton na siyasa ne sun buɗe musu wuta a Ofishin mazaɓarsa da ke Ilesa, jihar Osun yayin suke tsaka da gudanar da taro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin majalisar ya ce:

"Sai da jami'an tsarona suka jajirce matuƙa kafin su samu nasarar dakile nufin maharan, waɗanda da zuwansu suka bude wa Ofishina wuta lokacin ina ganawa da wata ƙungiya da safiyar jiya."
"Na samu labarin aikin wutar dan gudanar wanda na kashe sama da miliyan N15m a Oke-Aga na yi kaca-kaca da shi da harsasan bindiga. Ina jajantawa mutanen yankin da aka jefa cikin duhu saboda siyasar rashin hankali."

Musayar yawu ta barke tsakanin APC da PDP

Mai magana da yawun kwamitin kamfen Tinubu/Shettima na jihar Osun, Oluremi Omowaiye, ya zargi yan daban PDP da kashe mambobin APC 5 a Eti-Oni, karamar hukumar Atakumosa ta gabas.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bam Ya Tashi a Sakatariyar Karamar Hukuma a Arewacin Najeriya

Amma a nasa bangaren, shugaban kwamitin rikon kwaryan PDP, Akindele Adekunle, ya ce yan daban APC ne suka kai hari kuma suka kashe mambobin jam'iyarsa a Ilesa.

Premium Times ta ce a wata sanarwa da ya fitar, ya ce maharan sun yi ajalin mutum biyu yayin da na ukun ke kwance a Asibiti rai hannun Allah.

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Takarar Sanata da Wasu Mutane 5 Ana Saura Kwana 3 Zabe

Wasu 'yan bindiga sun harbe ɗan takarar Sanatan Enugu ta gabas na jam'iyyar LP tare da wasu magoya bayansa guda 5.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan harbe mutanen har lahira, yan ta'addan sun banka wa motar da suke ciki wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel