Gwamna Yahaya Bello Ya Ayyana Hutu Ga Ma'aikata Kan Ziyarar Buhari

Gwamna Yahaya Bello Ya Ayyana Hutu Ga Ma'aikata Kan Ziyarar Buhari

  • Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai kai ziyara jihar Kogi ranar Alhamis, 29 ga watan Disamba, 2022 don kaddamar da ayyuka
  • Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sanar da hutun wannan rana ga ma'aikatan jihar domin su karrama Buhari
  • Wannan dai itace ziyara ta farko da shugaban zai kai Kogi tun bayan hawan gwamna Yanaya Bello kan mulki a 2016

Kogi - Gwamna Yahaya Bello na jahar Kogi ya ayyana ranar 29 ga watan Disamba, 2022 a matsayin ranar hutu ga ma'aikatan jihar.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa gwamnan ya ayyana hutun ne sakamakon ziyarar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai kai jihar don kaddamar da wasu ayyuka.

Shugaba Buhari tare da Yahaya Bello.
Gwamna Yahaya Bello Ya Ayyana Hutu Ga Ma'aikata Kan Ziyarar Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa, Kingsley Fanwo, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Kirsimeti Lahadi 25 ga watan Disamba, 2022.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Ina Da Tabbacin APC Za Ta Lashe Zabe a Jihar Zamfara, Buhari

Sanarwan ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Shugaban kasa kuma kwamandan askarawan Najeriya, Muhammadu Buhari zai kawo ziyara ranar 29 ga watan Disamba, 2022, domin kaddamar da muhimman ayyukan raya ƙasa."
"Bisa la'akari da wannan da kokarin ganin an tarbi shugaban ƙasa, gwamnatin jihar Kogi karkashin gwamna Yahaya Bello tana mai sanar da cewa ta bayar da hutun ranar Alhamis, 29 ga watan Disamba."
"An ɗauki wannan matakin ne domin bai wa mutane damar tarbar mai girma shugaban ƙasa. Mina kira ga ƙungiyoyin mu na kwadugo da hukumomin tsaro sun tabbata komai ya tafi kan tsari da doka."

Gwamnatin Kogi ta kuma roki ɗaukacin al'ummar jihar da su fito kwansu da kwarwakata su nuna wa shugaban kasa karamcin da aka san su da shi.

"Gwamnati tana kira ga ɗaukacin al'umma su fito kwansu su tarbi shugaban ƙasa cikin karamcin da aka sansu da shi yayin da zai kaddamar da ayyukan raya ƙasa da zasu taimaki rayuwarsu."

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Gwamnan PDP Ya Rushe Ciyamomi 17, Mataimaka da Kansilolin Jiharsa

Ana tsammanin Buhari zai dira Kogi ranar Alhamis mai zuwa ziyara ta farko da shugaban zai kai tun bayan da Yahaya Bello ya karɓi mulki a 27 ga watan Janairu, 2016, daily trust ta ruwaito.

Na Kagara Na Koma Gida a Daura Nan Da Watanni 5, Shugaba Buhari

A wani labari kuma Manyan shugabannin Jam’iyyatu Ansaridden (Attijaniyya) sun ziyarci Shugaba Buhari a Abuja

Yayin wannan ziyara ne shugaban kasan ya yaba musu kana ya gaya musu ya kosa ya koma mahaifarsa Daura idan wa'adinsa ya kare a 2023.

Shehunnan Malaman sun yi nasiha tare da jan hankali kan koyi da rayuwar Annabi Muhammad SAW.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262