Na Kagara Na Koma Gida a Daura Nan Da Watanni 5, Shugaba Buhari

Na Kagara Na Koma Gida a Daura Nan Da Watanni 5, Shugaba Buhari

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yaba wa shugabannin ƙungiyar Tijjaniya bisa hakurin da suke sa wa a Addini
  • Shehunnan Malaman Tijjaniyya bisa jagorancin Sheikh Muhammad Khalifa Niass, sun kai wa Buhari ziyara yau a Abuja
  • Sheikh Niass ya jawo hankali kan bukatar koyi da halayen Manzon Allah SAW da yanayin rayuwarsa

Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya karɓi bakuncin mambobin ƙungiyar Jam’iyyatu Ansaridden (Attijaniyya) a fadarsa dake Abuja ranar Talata.

Shugaba Buhari ya kuma yabawa kungiyar Addinin Musuluncin bisa namijin kokarin da suke wajen hakurin a Addini.

Ziyarar Malaman Tijjaniyya.
Na Kagara Na Koma Gida a Daura Nan Da Watanni 5, Shugaba Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Shugaban ya shaida wa mambobin kungiyar karkashin jagorancin Sheikh Muhammad Khalifa Niass, Khalifan kungiyar cewa yana ganin ƙimar rawar da suke taka wa wajen samar da kwanciyar hankali a kasashen Afirka.

Haka zalika, Buhari ya gode masu bisa Addu'ar da suke wa gwamnatinsa mara iyaka da ma ƙasar nan baki ɗaya.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Da Okowa Sun Ziyarci Mahaifiyar Marigayi Yar'adua a Katsina, Hotunan Sun Ja Hankali

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Na kosa lokaci ya yi na koma Daura - Buhari

A wata sanarwa da Malam Garba Shehu, kakakin shugaban ƙasar ya fitar, Buhari yace ya ƙosa ya koma mahaifarsa Daura, nan da watanni 5 idan wa'adin mulkinsa ya cika.

Yayin ziyarar da malaman Musuluncin suka kai, Sheikh Tijjani Shehul Hadi Almauritany, ya yi Addu'a ga Buhari, Najeriya da mutanen cikin ƙasa yayin da Sheikh Abdullahi Lamine, ya yi karatun Alkur'ani.

Sheikh Niass ya yi nasiha

Da yake nasa jawabin, Khalifan ƙungiyar, Sheikh Niass, ya ja hankalin mutane kan rayuwar Manzon Allah, Annabi Muhammad SAW da kuma darussan da ya kamata musulmi su ɗauka a rayuwarsa.

Ya kuma jaddada bukatar yawan tuba ga Allah da yin Istigfari kamar yadda Littafin Allah mai tsarki Alƙur'ani ya koyar.

Sheikh Niass ya sha alwashin cewa ƙungiyar Tijjaniyya ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen inganta zaman lafiya da haɗin kai bisa tafarkin koyarwar Addinin Islama.

Kara karanta wannan

Rikicin APC Ya Dauki Sabon Salo, Majalisa Ta Tsige Ciyaman Daga Mukaminsa a Jihar Arewa

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya gana da shugaban majalisar wakilai kan muhimman batutuwan da suka taso

Femi Gabajabiamila, yace sun maida hankali kan sabon tsarin babban bankin Najeriya na takaita yawon kuɗi a hannu da kuma zaɓen 2023.

Wannan na zuwa ne awanni bayan gwamnan CBN ya sake aike wa mambobin majalisa da takardar ba zai samu zuwa gayyatarda suka masa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel