Atiku Ya Ce Shi Tsani Ne Ga Kabilar Igbo Dan Zama Shugaban Kasa

Atiku Ya Ce Shi Tsani Ne Ga Kabilar Igbo Dan Zama Shugaban Kasa

  • Atiku ya ziyarci tushen Inyamuran Nigeria, wato jihar Anambra ya gana da gwamna Carles Salodu
  • Wannan shine zuwan Aitku yakin Inyamurai karo na biyu tun bayan da ya ziyarci jihar Akwa-Ibom, duk dai a yakin neman zaben zaman shugaban kasar Nigeria a 2023
  • Ko a ziyarar tuntuba da Atikun yayi a jihar Ebony ya tabbatarwa da kabilar zai mika musu mulki in ya gama wa'adinsa

Anambra:Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce shi tsani ne ga kabilar Igbo wajen fitar da shugaban kasar Najeriya daga cikinsu.

Atiku, wanda ya yi magana a dandalin Alex Ekwueme, Akwa, a yayin taron gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a jihar Anambra, ya yi alkawarin taimakawa kabilar Igbo wajen fitar da shugaban kasa bayan wa’adinsa.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Zai Gana da Gwamnan Wata Jam'iyya da Sarakuna, PDP Ta Fara Kullin Shawo Kan Su Wike

“Zan zama matattakalar tabbatar da kabilar Igbo sun samu shugaban kasa muddin kuka zabe ni a 2023."
“Zaku iya tabbatar da hakan, in kun lura wannan shi ne karo na uku da zan yi takara da dan kabilar Igbo a matsayin Mataimakina."
"Idan da gaske kuna son samar da shugaban kasa, to ku zabi Atiku/Okowa," in ji shi.

Ya kuma yi alkawarin tabbatar da tashar gabar ruwan Onitsha ta fara aiki idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023. Rahotan Vanguard

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Atiku, wanda ya kai wa Gwamna Chukwuma Soludo ziyarar ban girma a Awka, ya bayyana gwamnan jihar Anambra, a matsayin amintaccen abokinsa, wanda zai hada kai dashi dan ciyar da Najeriya gaba idan aka zabe shi a 2023.

Ya ce dangantakarsa da Soludo ta wuce siyasar bangaranci, amma sun hadu a niyar yin gyare-gyare tare, dan bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa za mu zabi Tinubu a matsayin shugaban kasa – Kiristocin Kudu

Atiku
Atiku Ya Ce Shi Tsani Ne Ga Kabilar Igbo Dan Zama Shugaban Kasa Hoto: The Punch
Asali: UGC

Atiku ya kara da cewa:

“Wannan ya wuce siyasar jam’iyya. Kamata ya yi a samu matsaya kan yadda za mu ci gaba, kuma ni ina daukar gwamna Soludo a matsayin wanda muke da zuciya daya ta bunkasa Nigeria".
“Duk da bambance-bambancen da ke tsakaninmu na siyasa, ya kamata a sami wasu muhimman dabi'u da ya kamata mu amince da su wajen ci gaban kasarmu." inji Atiku
“Ina godiya ga Gwamna Soludo da bai rufe mana kofa ba, ya tarbe mu kuma ya bamu damar gudanar da kamfe dinmu lafiya."

Abinda Gwamna Soludu Yace

A nasa jawabin, Soludo ya ce ci gaban Najeriya ya kamata ya zama babban fifiko ga kowane dan siyasa ko dan takara.

A cewarsa Najeriya ta fi kowace jam’iyya girma kuma burin gina kasa ya fi kowane dan siyasa girma.

"A cikin wannan buri na gina Najeriya, Anambra da yankin Igbo su zama wata cibiya da za'a rinka kwakwayonta wajen bunkasa kasa da yanayin tattalin arziki".

Kara karanta wannan

Rikicin cikin gida: Abu daya zai sa na kada ma Atiku kuri'a ta a 2023, inji wani babban jigon PDP

"Na yi matukar farin ciki da kuka zo nan don yin yakin neman zaɓe , nayi imanin mutanenmu za su saurari duk wata magana da za ku gaya musu.
“Manufarmu ita ce mu sami daidaitontsakanin kowa da kowa. Siyasa ita ce ci gaba kuma muna son Kudu maso Gabas su samu wannan ci gaba.

Muna bukatar duk dan takarar da ya kai ga nasara da ya dubi aiyukan da gwamnatin tarayya ta fara tun daga zamanin mulkin shagari har zuwa yanzu, wanda ya kamata a karasa a karasa, wanda kuma za'a kirkira to a kirkiresu inji Solodu

Asali: Legit.ng

Online view pixel