Dalilin Da Yasa Za Mu Zabi Tinubu - Inji Kiristocin Kudancin Kasar Nan

Dalilin Da Yasa Za Mu Zabi Tinubu - Inji Kiristocin Kudancin Kasar Nan

  • Kungiyar Kiristocin kudancin Nigeria sun raba gari da dan takarar shugaban kasar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar
  • Amma Kungiyar Kiristocin Arewacin kasar nan ta sanar da marawa dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar Baya.
  • Kungiyoyi na addini dana kwararru na nuna goyan bayansu muraran ga yan takara sabida yadda suka yadda zasu biya musu bukatunsu ko kuma tabbatar musu da alkawarin da ke tsakaninsu

Imo: Kungiyar Kiristocin Kudancin Najeriya (SNCV) ta ce tana tunanin zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a 2023.

Sunce hakan wani abu ne da ke nuna cewa an raba tsarin mulki na tabbatar da ba dan arewa ne ya sake darewa akan mulki ba bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya bar mulki.

Kungiyar ta kuma yi gargadin cewa kada wasu su kuskura su yi Allah-wadai da wani dan takarar shugaban kasa da ya fito daga kowanne yanki, ko kuma addininsa ba.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Daukarwa Al'ummar Kaduna Da Arewa Wani Babban Alkawari Idan Har Ya Gaje Buhari

Da yake jawabi yayin taronsu a garin Owerri na jihar Imo, shugaban kungiyar Christian Vanguard ta kudancin Najeriya na kasa, Rev. Isaac Nwaobia ya bayyana cewa zai zama babban rashin adalci ga wani dan Arewa ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan shekaru takwas. Rahotan jaridar The Nation

Bola Tinubu
Dalilin Da Yasa Baza Mu Zabi Tinuba - Inji Kiristocin Kudancin Kasar Nan Hoto: This Day
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai Sanarwar Tasu Tace

Wata sanarwa da babban sakataren kungiyar Bishop Joseph Ajujungwa ya fitar, ta ruwaito Nwaobia na cewa hakan zai zama babban illa ga hadin kan kasar idan wani dan Arewa ya gaji Buhari.

“Tikitin tikitin musulmi-Musulmi ba shine abun ji ba yanzu ba. Abin da muke cewa shi ne, ya za a yi wani dan Arewa ya zo ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari a 2023 ba.
“Ina adalci, ina adalci? Dan Kudu ya kamata ya gaji Buhari domin kare hadin kan kasar."

Kara karanta wannan

Hotunan Yadda Yakin Neman Zaben Atiku/Okowa Ya Gudana Yau A Jihar Nasarawa

“Muna bukatar dan takarar kudanci ya yi nasara ba tare da la’akari da son zuciya ba.

Nwaobia ya nuna damuwarsa kan rashin tsaro a kasar, yana mai cewa hakan babbar barazana ce ga zabe mai zuwa.

“Yayin da yan makonni kadan ya rage ayi babban zaben kasa, babbar barazana a yanzu ita ce rashin tsaro. Babu inda ke da aminci a cikin ƙasa. Dole ne gwamnati ta tashi tsaye ta dauki matakan da suka dace don tabbatar da tsaron kafin babban zabe."

Ya ci gaba da cewa

"yace da'awarsu ta zaben Tinubu ba lalle ta wasu dade ba ko su suki yunkurin nasu, amma abinda muke so su sani shine ba san zuciya mukai ba" in ji shi.

Ya ce kungiyar za ta samar da kwakkwaran hadin gwiwa da hukumar zabe, yana mai cewa

"Zamu tabbatar da samun sahihan shugabanni dan tsame Nigeria daga halin kunchi, talauci da abubuwa da suka addabi Nigeria."

Asali: Legit.ng

Online view pixel