NNPP ta karyata jita-jitan ta kulla kawance da jam'iyyar PDP gabanin zaben 2023

NNPP ta karyata jita-jitan ta kulla kawance da jam'iyyar PDP gabanin zaben 2023

  • Jam’iyyar NNPP ta bayyana matsayarta game da hada kai da duk wata jam’iyyar siyasa a zaben 2023 mai zuwa
  • An yada wasu rahoranni da ke cewa, jam’iyyar NNPP ta hada kawance da jam’iyyar PDP gabanin zaben 2023
  • NNPP ta ce za ta yi kawance da kowa, amma dole sai dai a marawa dan takararta na shugaban kasa baya

Jam’iyyar NNP mai alamar kayan marmari ta su Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta ce bata kulla wata yarjejniyar kawance da jam’iyyar PDP ba, Leadership ta ruwaito.

Jam’iyyar ta ce ta ci karo da rahotannin da ake yadawa da ke cewa, sakataren kwamitin amintattun jam’iyyar, Buba Galadima ya kulla alakar kawance da tsakanin NNPP da PDP gabanin zaben 2023.

A cewar wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ta hannun sakataren yada labaranta, Major Agbo, NNPP ta ce babu wannan batu kuma bata ma san dashi ba.

Kara karanta wannan

Kasar Birtaniya Tayi Magana a Kan ‘Dan Takaran Shugaban Kasa da Za Ta Goyi Baya

NNPP bata hade da PDP ba, inji jigon jam'iyyar
NNPP ta karyata jita-jitan ta kulla kawance da jam'iyyar PDP gabanin zaben 2023 | Hoto: tostvnetwork.com
Asali: UGC

Matsayar jam'iyyar NNPP game da kulla kawance da wasu jam'iyyun siyasa

A cewar sanarwar:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Babu wannan shiri ko kadan a kasa kasancewar dan takararmu na shugaban kasa yana cikin wannan takara ne don ya yi nasara ya kuma samar da shugabanci mai ma’ana daidai da tsarin jam’iyyar.
“Ya shirya yin duk mai yiwuwa don nuna kwarewarsa a sha’awarsa ta yiwa ‘yan Najeriya hidima.
“A matsayin tarba mai yawa, NNPP na maraba da dukkan kawance na siyasa daga masu ra’ayi irin nata a manufarta ta ceto kasarmu amma tana kan matsayar dole duk wani yunkuri a yi shi ta yadda zai kai ga hada kai da dan takarar shugaban kasa Engr Rabiu Musa Kwankwaso ya yi nasara ba wai wata hanyar ba.”

Daga nan jam’iyyar ta karyata rahoton da ake yadawa, inda tace ba komai bane face rudu da wasu tsirarun jama’a ke yadawa a kasar nan, Tribune Online ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ga Atiku: Ka Zabtare Kudin Makaranta a Jami’arka ko ‘Yan Najeriya da Halarta

A mako mai zuwa ne jam'iyyar PDP za ta kai ziyarar kamfen jihar Anambra, tuni 'yan jihar da jiga-jigan jam'iyyar suka fara shirin tarbar Atiku.

Sun ce Atiku nasu ne na gida, don haka babu aiki a ranar, kamar yadda wata sanarwa ta bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel