Zaben 2027: Kitimurmurar da Ke a PDP da LP Ka Iya Zama Silar Nasarar Tinubu a Zabe Mai Zuwa

Zaben 2027: Kitimurmurar da Ke a PDP da LP Ka Iya Zama Silar Nasarar Tinubu a Zabe Mai Zuwa

  • A bayyane yake cewa jam'iyyun PDP da Labour na da kitimurmurar da rikice-rikice da dama da dole a warware su gabanin zaben shugaban kasa na 2027
  • Matukar bangarorin biyu ba su yi abin da ya kamata, akwai yuwuwar jam'iyyar APC za ta samu nasara cikin sauki a babban zaben na gaba
  • Yayin da jam’iyyar PDP ke fuskantar kitimurmurar cin dunduniyar jam’iyya, jam’iyyar Labour a halin yanzu na fama da wasu munanan batutuwan bangaranci

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Tsakanin zaben shugaban kasan da aka yi a 2023 zuwa yanzu, an ga abubuwa da yawa wadanda da alama za su yi tasiri ga wasu jam'iyyun siyasa a babban zabe mai zuwa na 2027.

Kara karanta wannan

“Bamu hana ka murabus ba”: Kungiyar kwadago ta fusata, ta tura sako mai zafi ga Peter Obi

Ga wasu jam'iyyun, kamar jam’iyyar PDP da Labour matsaloli ne da ke nasaba da yiwuwar raguwar damarsu ga kaiwa ga nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa a 2027.

Ga wasu kuma, kaamr APC da alama akwai lauje cikin nadi da ka iya kwancewa ya bayyana a fili duba da rabuwar kai da ke tsakanin shugabannin jam'iyyar da 'yan siyasar cikinta.

Wannan, ka iya zama silar dura ruwa a cikin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a zaben da a yanzu haka 'yan siyasar Najeriya sun fara shiri tsaf.

Yadda PDP da LP za su ba Tinubu dama a 2027
PDP da LP ka iya ba Tinubu damar nasara a 2027 | Hoto: Bola Ahmad Tinubu, Peter Obi, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsayar wannan rahoton

Wannan rahoton ya mai da hankali ne ga rikice-rikicen da ke cikin jam'iyyun PDP da Labour wadanda za su iya yin tasiri a gare su amma a karshe su zama silar nasara ga Shugaba Tinubu, idan ya yanke shawarar sake tsayawa takara a karo na biyu a 2027.

Kara karanta wannan

Yaki da garkuwa da mutane: 'Yan sanda sun yi ram da mutum 85 da ake zargin 'yan ta'adda ne

Tun kafin fara batun zabe, jam’iyyar PDP ta fara rasa matsayinta na babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, musamman a idon wasu masu sharhi kan harkokin siyasa.

A halin yanzu, kallo ya koma ga tsagin jam'iyyar adawa ta Labour duba da rikice-rikicen da ke cikin PDP.

Wadannan matsaloli dai ka iya zama silar rashin nasarar PDP a zabe mai zuwa da kuma disashewar haskenta a nan gaba kadan.

Yadda rikicin PDP ya fara a baya

Da farko dai, lamarin 'yan tawagar G-5 da suka hada da Nyesom Wike, Gwamna Seyi Makinde, Samuel Ortom, Okezie Ikpeazu da Ifeanyi Ugwuanyi, ya haifar da kakkausar gaba a PDP.

Alamu masu karfi na nuna cewa, jiga-jigan siyasar na ta rabar jam'iyyar APC tun gabanin zaben 2023, har ta kai Shugaba Tinubu ya ba Wike mukamin minista duk da kasancewarsa dan PDP.

Baya ga wannan, ana hasashen aukuwar ayyukan cin dunduniyar jam'iyyar PDP daga yankuna daban-daban na jam'iyyar a Najeriya, musamman jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Mafita mafi sauki: Reno Omokri ya ba 'yan Najeriya shawarin yadda za su shawo kan karyewar Naira

Hakazalika, a yanzu haka PDP za ta yi zama a ranar 18 ga watan Afrilu, kuma ana hasashen tsaiko tsakanin tsagin Atiku Abubakar da Nyesom Wike.

Wannan rikici ka iya zama wata kafar nasara ga Tinubu, kasancewar ya iya rabewa da 'yan jam'iyyun adawa; batun Wike ne misali mai karfi, rahoton jaridar Vanguard.

Bango ya tsage a jam'iyyar Labour

Ana ta samun kyawawan labarai masu dadi sosai daga jam'iyyar Labour tun bayan zaben shugaban kasa da ya gabata.

Sai dai, da farko, an samu tsagewar jam'iyyar zuwa bangaren Lamidi Apapa wanda ya dauki jam'iyyar zuwa wasu matakai don tabbatar da jajircewata a shekarar 2023.

Yayin da har yanzu ba a kai ga kashe wutar da ta kunno ba a jam’iyyar, akwai kuma wata wutar da ta kunno kan batun da ya shafi shugabancin Joe Ajaero da NLC, inda a yanzu shugabannin NLC suka ki amincewa da jagorancin Joe Ajaero wasu jiga-jigai

Kara karanta wannan

Adadin mutanen da aka kashe a harin Kogi ya karu, an roki Tinubu ya dauki mataki

Ya zuwa yanzu dai jam’iyyun PDP da Labour na da matsalolin da dole su warware kafin su iya fuskantar jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa mai zuwa nan da shekaru uku.

Duba karin rahotanni kan rikicin PDP da jam'iyyar Labour

Rikicin Labour da Peter Obi

A wani labarin kuma, kungiyar kwadago ta Najeriya ta shaida wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour cewa yana da ’yancin barin jam'iyyar ba wanda zai hana shi.

Kakakin kungiyar NLC, Benson Upah ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi dashi ranar Lahadi.

Shugabannin NLC sun sha alwashin cewa, ba za su huta ba har sai sun tsige Julius Abure a matsayin shugaban jam'iyyar Labour ta kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel