Ondo: Ƙanin Tsohon Gwamna Ya Samu Tikitin Takara, Zai Gyara Jihar a Shekara 1

Ondo: Ƙanin Tsohon Gwamna Ya Samu Tikitin Takara, Zai Gyara Jihar a Shekara 1

  • Kanin tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko ya yi nasarar samun tikitin takarar gwamna a zaben da za a gudanar
  • Abass Mimiko ya samu nasara a zaben fidda gwanin jam'iyyar ZLP da aka gudanar a yau Laraba 24 ga watan Afrilu
  • Yayin da ya ke jawabi bayan samun nasara, Abass ya ce zai fi ba da karfi bangaren ilimi da kiwon lafiya da kuma samar da tsaro a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Jam'iyyar ZLP ta sanar da wanda ya lashe zaben fidda gwani a zaben gwamnan jihar Ondo da za a gudanar.

Jam'iyyar ta sanar da cewa Abass shi ne ya yi nasara a zaben da aka gudanar a yau Laraba 24 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello bisa zargin karkatar da Naira biliyan 80

Kanin tsohon gwamna ya yi nasarar lashe zabe fidda gwani
Kanin tsohon gwamnan Ondo, Olusegun Mimiko ya samu tikitin tsayawa takarar gwamna. Hoto: Abass Mimiko.
Asali: Facebook

Takarar gwamna: Wasu alƙawura Mimiko ya yi?

Abass wanda kani ne ga tsohon gwamnan jihar, Olusegun Mimiko shi ne zai tsaya takarar gwamnan jihar a ranar 16 ga watan Nuwambar, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ya ke jawabi bayan samun nasarar, Mimiko ya ce zai mayar da hankali kan kiwon lafiya da tsaro da kuma ilimi idan ya yi nasara.

Likitan wanda ya shiga harkar siyasa ya ce a cikin shekara daya na mulkinsa, zai tabbatar ya samar da wadataccen abinci ga al'umma, cewar rahoton Vanguard.

"Zamu tabbatar da samar da wadataccen abinci a jihar Ondo da kuma inganta ilimi."
"Daga cikin tsare-tsarenmu akwai inganta harkokin kiwon lafiya da bunkasa tattalin arziki da samar da gidaje a jihar."

- Abass Mimiko

Abass ya ce tsohon gwamnan jihar ya na goyon bayansa dari bisa dari duk dabambancin jami'yya da suke da shi a jihar.

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Wanene zai lashe zaben fidda gwanin kujerar gwamna a jam'iyyar PDP?

APC ta sanar da ɗan takararta a Ondo

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta kammala zaben fidda gwani da aka gudanar a jihar Ondo.

Jam'iyyar ta ayyana Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda zai tsaya mata takarar gwamna a zaben watan Nuwamba.

Shugaban kwamitin zaben jihar, Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi shi ya tabbatar da haka bayan kammala zaben mai cike da rikici.

Asali: Legit.ng

Online view pixel