Yadda Na Zama ‘Dan Takaran Majalisa Alhali Ina Hannun ‘Yan Bindiga – Sadiq Ango

Yadda Na Zama ‘Dan Takaran Majalisa Alhali Ina Hannun ‘Yan Bindiga – Sadiq Ango

  • Hon. Sadiq Ango Abdullahi yana cikin wadanda aka yi garkuwa da su a jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja
  • Amma duk da haka, Sadiq Ango Abdullahi ya lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP a Kaduna
  • ‘Dan siyasar yace mutanensa na gidan siyasa suka rike masa amana, har ya yi nasarar samun tikitin PDP

Abuja - Sadiq Ango Abdullahi ya yi bayani a game da yadda ya yi nasarar zama ‘dan takarar majalisar wakilan tarayya a lokacin da yake tsare.

Hon. Sadiq Ango Abdullahi ya zama ‘dan takara ne a yayin da yake hannun ‘yan bindigan da suka yi garkuwa da su a jirgin kasan Kaduna-Abuja.

Da aka yi hira da shi a gidan yada labarai na BBC Hausa, ‘dan siyasar yace nasararsa ta rataya ne a kan mutane masu amana da ya mora a siyasa.

Idan har ya yi nasara a karkashin jam’iyyar PDP a babban zabe na shekara mai zuwa, Ango Abdullahi zai wakilci mazabar Sabon Gari a jihar Kaduna.

Ba abin mamaki ba ne - Ango

"Na samu cin zabe duk da ba na nan, dalilin wancan ibtila’i da ya same ni na sace ni da aka yi, amma cikin hukuncin Allah, na cin zaben duk da haka

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ba abin mamaki ba ne duk da haka gaskiya, saboda muna tare da wasu mutane ‘yan amana. Akwai sunayen mutane da-dama wadanda zan iya kira daga nan.
Sadiq Ango
Sadiq Ango Abdullahi Hoto: (Sadiq Ango Abdullahi)
Asali: Facebook

Matashin ya fadawa BBC Hausa cewa muddin akwai yarda tsakanin ‘dan siyasa da magoya bayansa, za suyi masa aiki domin ya taimakawa al’umma

Sadiq Ango Abdullahi yace a haka jama’ansa na siyasa suka tsaya masa har ya samu takara a jam’iyyar PDP da sa ran idan ya fito zai cigaba da fafutuka.

"A duk zaben fitar da gwani, ana haduwa da masu tsaida ‘dan takara da shugabannin jam'iyya. Duk da ba na nan, akwai mutanena da suke aiki dare da rana domin cin ma burinmu na taimakawa al’umma.
Mutane sun yi abin da ya kamata, ba abin na yi tunani zan fito in gani ba ne, amma da na gani ban yi mamaki ba domin na san su wanene suka yi wannan aiki, zan yi amfani da damar nan, in kara gode masu."

- Sadiq Ango Abdullah

Idan Ango ya je majalisa, me zai yi?

‘Dan siyasar yace nasararsa za ta wayar da kan al’umma cewa matashi ya fi cancanta ya rike mukami domin shi ya san matsalar ‘danuwansa matashi.

A hirar da aka yi da shi BBC, Sadiq Ango Abdullahi yace mai jini a jika ne zai yi aiki ba tare da ya gaji ba. Ango yana sa ran maye gurbin Garba Datti Babawo.

Daga barin APC, ya samu takara a PDP

An ji labari kwanaki cewa a zaben fitar da gwanin 'dan majalisar tarayya na Sabon Gari a Kaduna, Sadiq Ango ya zo na farko duk da bai dade da shiga PDP ba.

Ango Abdullahi ya samu kuri’a 28, yayin da Hajiya Hadiza Muhammad. Salisu Abdulhamid da wata Misis Pauline suka zo na biyu, uku da na hudu a zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel