Mai neman takara ya samu tikitin PDP yayin da yake hannun masu garkuwa da mutane

Mai neman takara ya samu tikitin PDP yayin da yake hannun masu garkuwa da mutane

  • Sadiq Ango Abdullahi ya samu galaba a kan ‘yan takarar majalisar wakilan tarayya a Sabon Gari
  • Idan abubuwa sun tafi daidai, Ango Abdullahi ne zai yi wa PDP takarar ‘dan majalisa a zaben 2023
  • Har zuwa yanzu babu tabbacin cewa matashin ‘dan siyasar ya bar hannun ‘yan garkuwa da mutane

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Sadiq Ango Abdullahi ne wanda ya samu nasara a zaben tsaida gwani da jam’iyyar PDP ta shirya a karamar hukumar Sabon Gari, jihar Kaduna.

A ranar 23 ga watan Mayu 2022, jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Sadiq Ango Abdullahi ya tika sauran masu neman takara a jam’iyyar PDP da kasa.

Rahoton ya ce a zaben fitar da gwanin da aka gudanar jiya, Ango ne ya zo na farko, ya doke sauran abokan hamayyarsa duk da bai dade da shiga jam'iyyar ba.

Kara karanta wannan

Takarar ‘Dan Gwamna El-Rufai a 2023 ta yi waje da ‘Dan Majalisan Kaduna daga Jam'iyyar APC

Ango Abdullahi ya samu kuri’a 28, yayin da Hajiya Hadiza Muhammad. Salisu Abdulhamid da Misis Pauline ne suka zo na biyu, uku da na hudu a zaben.

Hakan ya na nufin Sadiq Ango Abdullahi shi ne wanda zai yi wa jam’iyyar PDP takara a mazabarsa ta Sabon Gari da ke garin Zaria a zabe mai zuwa.

Ya na hannun miyagu?

Sai dai har zuwa yanzu Sadiq Ango Abdullahi yana cikin mutum 61 da aka yi garkuwa da su a jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja tun a karshen watan Maris.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sadiq Ango Abdullahi
Hon. Sadiq Ango Abdullahi Hoto: (Sadiq Ango Abdullahi)
Asali: Facebook

Har zuwa yanzu da mu ka samu rahoton nan, babu tabbacin ‘dan siyasar ya kubuta. Kwanaki aka yi ta rade-radin cewa ya fito, amma babu wanda ya gan shi.

Legit.ng Hausa ta tuntubi wasu na kusa da Ango Abdullahi a garin Zaria, amma duk sun shaida mata cewa babu gaskiya a labarin fitowarsa da ake ta yadawa.

Kara karanta wannan

An shiga rudani, wasu sun 'sace' masu kada kuri’a wajen zaben tsaida ‘Yan takaran PDP

A wani kaulin kuma, an bayyana cewa mai neman takarar ya bar hannun ‘yan bindiga bayan an biya kudin fansa, ya wuce kasar waje domin a duba lafiyarsa.

Mahaifinsa, Farfesa Ango Abdullahi ya tabbatar da cewa Sadiq yana hannun wadanda suka yi garkuwa da shi, amma su na sa ran cewa za a kubutar da shi.

Siyasar Sadiq Ango Abdullahi

A 2015 ne Sadiq Ango ya fara fitowa neman takarar kujerar majalisar wakilai a karkashin APC, amma Hon. Garbi Datti Mohammed ne ya samu tikitin jam’iyya.

Daga baya ya sake neman tikitin jam’iyyar mai mulki amma bai dace ba a 2019. A shekarar nan ya fice daga APC zuwa PDP da nufin ya samu takara a zaben 2023.

Sadiq Ango yana da farin jini a wajen matasan yankin Zaria. Mahafiyarsa ita ce Marigayi Sanata Aisha Jummai Alhassan, mahaifinsa kuma Farfesa Ango Abdullahi.

Samaila Sulaiman ya samu takara

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hatsarin mota ya rutsa da dan takarar gwamnan APC a Abuja

Dazu kun ji labari Samaila Suleiman ya samu tikitin jam'iyyar PDP da kuri’u 20 bayan doke Shehu Usman ABG da kuma Baffa Namadi Sambo masu kuri’u 14 da 2.

Suleiman ya yi nasara a zaben fitar da gwanin da aka shirya a ranar Lahadi. Idan ta tabbata, zai yi takarar majalisar wakilan tarayya na yankin Arewacin Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel