Ku Zabi PDP, Mun Yi Muku Tanadi Mai Kyau a 2023, Inji Jigon Jam’iyyar a Delta

Ku Zabi PDP, Mun Yi Muku Tanadi Mai Kyau a 2023, Inji Jigon Jam’iyyar a Delta

  • Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa, akwai shirye-shiryen ci gaba da take dashi ga 'yan Najeriya idan Atiku Abubakar ya lashe zaben 2023
  • PDP ta ce, 'yan Najeriya na ci gaba da fuskantar kalubale daga hannun jam'iyyar PDP tun bayan zaben 2015 da ta samu mulki
  • Kungiyar MURIC ta ce ya zama wajibi ga dukkan Musulmi Bayarbe ya zabi Bola Ahmad Tinubu a zaben 2023

Jihar Delta - Jam'iyyar PDP a jihar Delta ta tabbatarwa 'yan Najeriya cewa, akwai gobe mai haske ga kasar nan matukar ta samu damar komawa mulki bayan zaben 2023, Vanguard ta ruwaito.

Wannan na fitowa ne daga bakin mataimakin shugaban jam'iyyar a mazabar Delta ta Arewa ta majalisar dattawa, Mrs Moses Iduh, inda yace 'yan Najeriya suna shan fama hannun APC.

Ya kuma bayyana cewa, PDP na fatan samun nasara a 2023 domin ceto Najeriya daga halin da take ciki, inda ya bukaci jama'ar yankinsu da su zabi jam'iyyar a zabe mai zuwa.

PDP ta fadi tanadinta ga 'yan Najeriya
Ku Zabi PDP, Mun Yi Muku Tanadi Mai Kyau a 2023, Inji Jigon Jam’iyyar a Delta | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A yi PDP dodar, inji shugabannin jam'iyyar

Sakataren gidan gwamnati, kuma kodinetan kamfen na PDP a Oshimili ta Arewa, Chief Patrick Ukah ya bukaci jama'a da su ba da kuri'unsu ga Atiku da Okowa da kuma dan takarar gwamnan jihar, Sheriff Oborevwori da sauran 'yan takarar PDP a fadin kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ukah ya ce, PDP za ta mai da hankali wajen inganta ababen more rayuwa da zuba hannun jari kan jama'a a jihar Delta da ma sauran yankuna.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, shugabar tawagar kamfen ta yankin Oshimili ta Arewa, Princess Pat Ajudua, kwamishinan filaye na jihar, Chief Kate Onianwa da shugaban karamar hukumar Oshimili ta Arewa, Mr Innocent Esewezie sun yaba da abin da gwamna Okowa ya cimma cikin shekaru 7.

A cewarsu, yankin Ibusa na nan a turbar PDP tun 1999, kuma suna fatan hakan ya ci gaba har zuwa nan gaba.

PDP ta yi gangami mai cike da dimbin maso, ya kuma samu halartar jiga-jigai a jihar ta Delta.

Jam'iyyun siyasa na ci gaba da tallata 'yan takara gabanin babban zaben 2023 da ke tafe nan ba da dadewa ba.

Wajibi ne Musulmi ya zabi Tinubu, inji MURIC

A bangare guda, APC na ci gaba kokarin komawa mulki a 2023, kungiyar kare hakkin Musulmai ta MURIC ta ce dole ne Yarbawa Musulmai su zabi Tinubu.

Kungiyar ta bayyana dalilinta na fadin da cewa, sam 'yan yankin Kudu maso Yamma basu da zabin da ya wuce su zabi APC.

Kungiyar ta kuma ce, yankin bai taba samun wakilcin Musulmi Bayarbe ba tun kafin 1999 da PDP ta fara muki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel