Dole Ne Musulman Kudu Maso Yamma Su Goyi Bayan Tinubu, Inji MURIC

Dole Ne Musulman Kudu Maso Yamma Su Goyi Bayan Tinubu, Inji MURIC

  • Kungiyar kare hakkin Musulmai a Najeriya ta bayyana dan takarar da ya kamata Musulmai su zaba a zaben 2023 mai zuwa
  • Shugaban kungiyar ya ce, Bola Ahmad Tinubu ne ya fi cancanta a zaba a matsayin wanda zai gaje Buhari duba da wasu dalilai
  • Kungiyoyi da jiga-jigan kiristan Arewa na ci gaba da nuna adawa da yadda Tinubu ya zabi Kashim Shettima a matsayin abokin takara

Ibadan, jihar Oyo - Kungiyar kare hakkin Musulmai ta MURIC ta bayyana cewa, Musulmai a Kudu maso Yamma ba su da zabin da ya wuce su zabi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu a zaben 2023.

Daraktan MURIC, farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin da yake zantawa da manema labarai a jami'ar Ibadan kan batutuwan da suka shafi zaben 2023.

Kara karanta wannan

Atiku: Zan Fitar Da Sunayen Ɓarayin Man Fetur, Zan Kunyata Su Idan An Zabe Ni Shugaban Ƙasa A 2023

Akintola ya shaida cewa, Musulmai Yarbawa a kasar na sun sha fama na tsawon lokaci na rashin wakilci a sama, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ya kuma kara da cewa, dukkan wadanda suka yi shugabancin kasar nan ko rike kujerun mataimakin shugaban kasa kiristoci ne daga yankin.

MURIC ta ce babu zabi ga Musulmai sai su zabi Tinubu
Dole Ne Musulmai Kudu Maso Yamma Su Goyi Bayan Tinubu, Inji MURIC | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Saboda haka ne Akintola yace tabbas Musulman yankin ba su da zabin da wuce su zabi dan uwansu Musulmi, wato Bola Tinubu.

Zabin Musulmin Kudu maso Yamma shi ne su zabi Tinubu a 2023, inji Akintola

A cewarsa, dalilin da yasa ya yi wannan kira ba komai bane face cewa, Tinubu ne dan takarar shugaban kasa Musulmi da ya fito daga yankin Kudu maso Yamma a iya saninsa.

Da yake tsokaci game da gamin Tinubu da Shettima, Akintila ya ce, hakan ba komai bane face kaddara da ta riga fata, inda ya kara da cewa, ya kamata kowa a Najeriya ya zabi Tinubu, rahoton ICIR.

Kara karanta wannan

2023: Tun da ‘Dan takaransa ya sha kashi, Buratai ya nuna wanda yake goyon baya

Kafin wannan, kungiyar kiristocin Najeriya ta sha nuna damuwa da yadda Bola Ahmad Tinubu ya zabo Musulmi a matsayin abokin takararsa a zaben 2023 mai zuwa.

Duk da kungiyar CAN ta gana da Tinubu ta kuma bayyana masa bukatunta, har yanzu akwai kungiyoyin kirista da jiga-jigan siyasar nan da ke ganin ba za su yi Tinubu ba badi.

Wani batu ya ma bayyana cewa, zai yi wuya Tinubu ya iya cika biyu daga cikin bukatu bakwai da CAN ta bayyana masa.

Shi ma da yake tsokaci game da gamin Tinubu da Shettima, Akintila ya ce, hakan ba komai bane face kaddara da ta riga fata, inda ya kara da cewa, ya kamata kowa a Najeriya ya zabi Tinubu, rahoton ICIR.

Asali: Legit.ng

Online view pixel