Gaskiyar Magana Game da Jita-Jitar Atiku Zai Janye Daga Takarar Shugaban Kasa 2023

Gaskiyar Magana Game da Jita-Jitar Atiku Zai Janye Daga Takarar Shugaban Kasa 2023

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP, Atiku Abubakar, ya karyata raɗe-raɗin cewa ya fara tsorata zai janye daga tseren 2023
  • Mai magana da yawunsa, Paul Ibe, yace kamata ya yi a duba masu yaɗa irin wannan karerayi mai yuwuwa suna shaye-shaye
  • An fara yaɗa cewa Atiku na tunanin aje tikitin PDP sakamakon rashin gamsuwa da kamfe da rikicin cikin gida

Abuja -Mai magana da yawun, Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP, Paul Ibe, ya zargi jam'iyya mai mulki da kokarin tada rikicin siyasa.

Jaridar Punch ta rahoto Mista Ibe na cewa irin wannan halayyar da APC ke nuna wa ta fito a zahiri kowa ya gani a lokacin gangamin kamfen Atiku na Borno da Kaduna.

Atiku Abubakar.
Gaskiyar Magana Game da Jita-Jitar Atiku Zai Janye Daga Takarar Shugaban Kasa 2023 Hoto: punchng
Asali: Twitter

Bayan haka ya yi fatali da raɗe-raɗin dake ikirarin cewa Atiku ya fara tunanin janye wa daga takarar shugaban ƙasa saboda ya gaza warware rigingimun PDP musamman da G5.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Wasu Gwamnoni Sun Kama Hanyar Ficewa Daga PDP? Atiku Ya Yi Magana

Daga ina jita-jitar janyewa ta taso?

Wani mai amfani da kafar Twitter, Cousin Ray, ya yi ikirarin cewa wata majiya ta jikin Atiku ta gaya masa ɗan takarar ya yi matuƙar ɗaukar zafi bisa rashin gogewar kamfe da kuma rigingimun cikin gida.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ray ya ƙara da cewa ɗan takaran ya faɗa wa makusantansa cewa baya son sake san kayen raba ni da yaro a babban zaɓen 2023, dan haka zai maida wuƙarsa kube.

Gaskiyar lamarin

Sai dai da yake martani kan batun, Mista Ibe ya yi tantamar cewa anya mutanen dake da hannun a yaɗa wannan karerayin ba su shan wasu kwayoyi kuwa.

Yace:

"Ina ganin muna bukatar mu binciki waɗannan mutanen ko suna shaye-shaye, wace kwaya suke haɗiya, kun ji abinda gwamna Wike da takwaransa Ortom suka faɗa. Abu ne a fili, mai gidan gilashi ba zai yi wasan jifa ba."

Kara karanta wannan

2023: Na Gano Matsalar Najeriya, Abu Ɗaya Ne Tal, Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Magantu

"Ina baku tabbacin cewa duk taƙaddamar dake faruwa a PDP zamu warwareta saboda sun fara jan hankali, a yanzu sun ɗauki hanyar fara kamfe."

Ya kuma zargi APC da yaɗa farfaganda, inda ya ce, "APC jam'iyya ce wacce ta ɗauki tada rikici al'ada, sun tada yamutsi a Borno kuma haka suke a kowane mataki, jiha da tarayya."

A wani labarin kuma Adams Oshiomhole Ya nuna goyon bayansa ga tsagin Wike G5 a rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP

Tsohon shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa yace shugabanci na bukatar nuna halin dattako, idan an yi yarjejeniya a cika.

Oshiomhole, wanda ya kafa hujja da matsayar da gwamnonin kudu suka cimma a Asaba, yace Wike ne gwarzonsa na shekara sakamakon tsayawarsa kai da fata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel