Tsohon Shugaban APC Ya Tsoma Baki a Rigimar Atiku da Wike, Ya Goyi Bayan Daya

Tsohon Shugaban APC Ya Tsoma Baki a Rigimar Atiku da Wike, Ya Goyi Bayan Daya

  • Tsohon gwamnan jihar Edo na zango biyu, Adams Oshiomhole, yace gwamna Wike ke kan gaskiya a takaddamar PDP
  • Tsohon shugaban APC na ƙasa yace shugabanci na bukatar nuna hali mai kyau ba wai ana ɗaukar alƙawari kuma a warware ba
  • Wike ya gayyaci Oshiomhole zuwa jihar Ribas ne domin ya kaddamar da wata gadar sama da ya gina

Rivers - Yayin da taƙaddamar jam'iyyar PDP taƙi cinyewa, tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Adama Oshiomhole, ya nuna cikakken goyon bayansa ga fafutukar tsagin gwamna Wike na jihar Ribas.

Oshiomhole ya bayyana matsayarsa ne ranar Laraba a wurin kaddamar da katafariyar gadar saman Rumuepirikom a ƙaramar hukumar Obio-Akpor, jihar Ribas.

Oshiomhole da Wike.
Tsohon Shugaban APC Ya Tsoma Baki a Rigimar Atiku da Wike, Ya Goyi Bayan Daya Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

A cewarsa, shugabanci na nufin kyakkyawan hali ba wai a rinƙa yarjejeniyar da ansan ba za'a cika ba, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Na Yi Nadama Ka Yafe Ni" Gwamna Wike Ya Roki Afuwar Tsohon Shugaban APC Kan Abu Ɗaya

Oshiomhole, wanda ya rike kujerar gwamnan jihar Edo tsakanin 2008 zuwa 2016, ya amsa gayyatar da gwamna Wike ya masa ne na zuwa kaddamar da aiki a Ribas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Mako biyu da suka gabata na yi wata hira kuma wani ya tambayeni menene hange na game da taƙaddamar dake faruwa a PDP mai alaƙa da mai girma gwamna (Wike)."
"Na faɗa masa Wike ne gwarzona na shekara saboda ya tsaya kai da fata cewa Siyasa ba ɗaukar alƙwarin da ba za'a cika ba, shugabanci na bukatar halayya mai kyau."

Tsohon shugaban APC ya haƙaito lokacin da gwamnoni 17 na kudancin Najeriya suka zauna a Asaba, jihar Delta ranar 11 ga watan Mayu, 2021 suka yanke cewa ya kamata magajin Buhari ya fito daga kudu.

A cewarsa, wannan matsayi da gwamnoni daga dukkanin jam'iyyu suka ɗauka daga zuciyarsu ya fito kuma sun haɗa kai kan yankin da zai ba da shugaban kasa na gaba.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Tsohon Shugaban APC Ya Dira Patakwal Yayin da Wike Ya Cigaba da Ɗasawa da Jiga-Jigan APC

"Idan kuka cimma matsaya a koda yaushe ana tsammanin cikata. Idan kuka watsar da yarjejeniyar amma wani yace ni ina nan kan wannan yarjejeniya, menene kuskurensa?"

Mambobin PDP Sun Yi Wa Filin Da APC Ta Kaddamar Da Yakin Neman Zabenta a Jos Wankan Tsarki

A wani labarin kuma awanni bayan kammala taro, wasu tawagar mambobin PDP sun wanke filin taron da jam'iyyar APC ta gudanar da yaƙin neman zaɓe a Jos

Rahotanni sun nuna cewa mazauna Jos babban birnin jihar Filato musamman maau goyon bayan PDP sun je filin wasan kana suka sa ruwa suka wanke shi.

Ƙungiyoyin da suka haɗa kai mutanen sun bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da aniyarsa na fatattakar APC daga jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel