Nasara Na Tattare Da Tinubu Bayan Wani Gwamnan Yakin Kudu Maso Gabas Ya Mara Masa Baya

Nasara Na Tattare Da Tinubu Bayan Wani Gwamnan Yakin Kudu Maso Gabas Ya Mara Masa Baya

  • Bola Ahmed Tinubu a halin yanzu yana kama da wanda ba za a iya cece-kuce ba a takarar shugaban kasa
  • Tsohon gwamnan na Legas ya sake samun wani babban goyon baya daga yankin kudu maso gabas inda takwaransa Peter Obi ya fito
  • Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya ce zai gudanar da wani gagarumin gangami na jam'iyyar APC.

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sake samun tagomashi sakamakon samun goyon baya daga yankin kudu maso gabashin Najeriya. kamar yadda jaridar Legit.ng ta hakaito

Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya ce al’ummar sa za su fito kwansu da kwarkwata domin marawa takarar shugaban kasar Tinubu baya tare da tabbatar jihar sa ta rike kambunta wajen marawa jam’iyyar APC baya.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Ya Sa Arewa Ke Goyon Bayan Tinubu, Sanata Mai Karfin Fada A Ji A APC Ya Magantu

Kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito, Gwamna Umahi ya bayyana haka a ranar Laraba, 16 ga watan Nuwamba a Abuja a wajen kaddamar da masaukin gwamnan jihar Ebonyi a babban birnin tarayyar kasar.

TINUBU
Nasara Na Tattare Da Tinubu Bayan Wani Gwamnan Yakin Kudu Maso Gabas Ya Mara Masa Baya Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamna Dave Umahi Ya Yi Alkawarin Daukar Nauyin Duk Wani Kamfen Din Tinubu A Ebonyi

Yace:

“Za mu yi gangamin da ba a taba ganin irinsa ba a yankin Kudu maso Gabas a Jihar Ebonyi. Duk jam’iyyar da ta zo Ebonyi, da zata iya samun kashi 10 cikin 100 na al’ummarta, kuma zamu raba sauran kuri’un kashi goman yayin da sauran kuma na APC ne.
“A matsayina an shugaban gwamnonin kudu maso gabas zanyi amfani da wannan damar tare da kawar da duk wanda zai fake damu dan ganin ya kawo ma cikasa a kudirinka ko kuma yunkurin da jam'iayyarmu ta APC ke na sake darewa kan karagar mulki"

Kara karanta wannan

Mutanen Jihata Zasu Angiza Wa Tinubu Tulin Kuri'unsu, Atiku Bai da Rabo, Gwamna Ya Magantu

Gwamna Umahi ya ci gaba da bayyana cewa zai yi amfani da ikonsa a matsayinsa na shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas domin tabbatar da nasarar Tinubu a yankin.

Yace:

“Don haka mutanen Kudu-maso-Gabas, mun yi magana. Ni ne Shugaban kungiyar Gwamnonin Kudu maso Gabas don haka, ina magana a madadinsu. Mun san inda zai fi mana kyau a 2023 kuma ita ce APC."

An Gurfanar Da Shugaban NURTW Saboda Lalata Allon Tallan Tinubu a Jihar Babban Jihar PDP

An gurfanar da Mukaila Lamidi, da aka fi sani da Auxilliary, shugaban haramtaciyar kungiyar direbobi NURTW na jihar Oyo a kotu kan lalata allon kamfen din Bola Tinubu, The Nation ta rahoto.

Bola Tinubu shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023 kuma jam'iyyar PDP ce ke mulki a Oyo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel