Mutanen Ebonyi Zasu Yi Tururuwar Zaben Bola Tinubu a 2023, Gwamna Umahi

Mutanen Ebonyi Zasu Yi Tururuwar Zaben Bola Tinubu a 2023, Gwamna Umahi

  • Gwamnan Ebonyi ya sha alwashin cewa baki ɗaya mutanen jiharsa zasu dangwala wa Bola Tinubu a 2023
  • Dave Umahi, ya tabbatar wa ɗan takarar APC cewa zai ga aikin Injiniya duk ranar da ya je Kamfe jihar Ebonyi
  • Yace a madadin gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya sun yanke mara wa Tinubu baya domin zai kula da mutanen yankin

Abuja - Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya tabbatarwa ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Tinubu, cewa jiharsa zata ba shi ƙuri'u masu yawa a 2023.

Umahi ya yi wannan furucin ne a wurin kaddamar da gidan saukar gwamnan Ebonyi a Abuja ranar Laraba, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Gwamna Umahi da Bola Tinubu.
Mutanen Ebonyi Zasu Yi Tururuwar Zaben Bola Tinubu a 2023, Gwamna Umahi Hoto: channelstv
Asali: Twitter

Ya kuma bayyana cewa jihar da ke shiyyar kudu maso gabashin Najeriya na shirya masa wani gagarumin gangamin yakin neman zaɓen shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Kamfen Jos: Dalilin da Ya Sa Zan Taimakawa Tinubu Ya Gaji Kujerata a 2023, Shugaba Buhari

A ruwayar Vanguard, Umahi yace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Zamu shirya gangamin da ba'a taɓa gani ba a kudu maso gabas a jihar Ebonyi kaɗai. Duk wata jam'iyya da ta iya samun kashi 10 na kuri'un mutanenmu zamu ƙara musu da wasu saboda ba jam'iyyar da zata iya."
"Saboda haka muna maraba da Tinubu da sauran gwamnonin zuwa jihar Ebonyi wurin uwar gangami. Ranka ya daɗe zaka ga abinda Injiniya zai iya yi idan ka zo.

Baki ɗaya kuri'un Ebonyi naka ne - Umahi

"Bamu ɓoye cewa kai ɗan takararmu ne kuma zaka kula da mutanen kudu maso gabas, kuri'unmu duka na APC ne babu tantama a kan haka, mutanen kudu maso gabas sun ɗau matsaya."
"Ni ne shugaban ƙungiyar gwamnonin kudu maso gabas, ina magana ne a madadin su, mun san hanyar da zata ɓulle mana a 2023 kuma ita ce APC."

Kara karanta wannan

Tinubu: Zan Kora Wani Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Koma Mahaifarsa a 2023, Ya Faɗi Suna

- Dave Umahi.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa taron ya samu halartar tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu da wasu mambobin jam'iyya mai mulki.

A wani labarin kuma daga wurin gangamin kamfen Tinubu na Jos, Yahaya Bello ya sha alwashin tattara wa Tinubu matasan Najeriya a zaɓen 2023

Da yake nasa jawabin, gwamnan jihar Kogi, Ko'odinetan matasa, yace mulkin APC tun zuwam Buhari ya ɗaga daraja da ƙimar Najeriya a idon duniya

Gwamnan yace sakamakon ayyukan raya ƙasa da shugaba Buhari ya aiwatar, Najeriya ta kere ƙasashe da dama ciki harda waɗanda suka cigaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel