Gwamnonin PDP Da Suka Bayar Da Sharudda A Bainar Jama'a Kafin Yi Wa Atiku Aiki A Jihohinsu

Gwamnonin PDP Da Suka Bayar Da Sharudda A Bainar Jama'a Kafin Yi Wa Atiku Aiki A Jihohinsu

  • Jam'iyyar PDP da rikici sun zama tamkar mata da miji tun bayan da Atiku ya zama dan takarar shugaban kasa a watan Mayu
  • Wasu masu karfin fada a ji a jam'iyyar na ganin sakamakon zaben fidda gwanin ya ci karo da kiran da aka yi na cewa mulki ya koma kudu, hakan yasa aka gaza samun zaman lafiya a jam'iyyar
  • Amma, wasu daga cikinsu sun bude kofar sulhu kuma sun bada sharudda idan ana son su goyi bayan Atiku Abubakar, wanda bisa alamu ba zai cika musu ba

Jam'iyyar PDP ta tsinduma cikin rikici tun bayan da Atiku Abubakar ya yi nasarar zama dan takarar shugaban kasa na zaben 2023.

Saboda tsadar rayuwa da wasu matsalolin, wasu yan kasar na goyon bayan jam'iyyar hamayyar ta kwace mulki daga APC a zaben da ke tafe.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Kama Mutum 12 Dake da Hannu A Kaiwa Magoya Bayan Atiku Hari

Atiku da gwamnonin PDP
Gwamnonin PDP 3 Da Suka Bayar Da Sharudda A Bainar Jama'a Kafin Yi Wa Atiku Aiki A Jihohinsu. Hoto: Photo Credit: Atiku Abubakar, Seyi Makinde, Nyesom Wike
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Halin da ake ciki tsakanin Atiku Abubakar na PDP da kungiyar gwamnonin G5

Duk da kirarin da ake yi wa Atiku na mai hada kawunan mutane, kawo yanzu ya gaza hada kan jam'iyyar ta PDP.

Gwamnonin jihohin Ribas, Benue, Abia, Oyo da Enugu, wanda ake kira G5 sun neman shugaban jam'iyyar Iyorchia Ayu ya sauka don a bawa dan kudu mukaminsa, abin da suka kira adalci da daidaito a shugabancin jam'iyyar.

Manyan gwamnonin 3 da suka bada sharuddan goyon bayan Atiku sune:

1. Samuel Ortom na Benue

2. Nyesom Wike na Ribas

3. Seyi Makinde na Oyo

Samuel Ortom

Samuel Ortom
Gwamnonin PDP Da Suka Bayar Da Sharudda A Bainar Jama'a Kafin Yi Wa Atiku Aiki A Jihohinsu
Asali: UGC

Gwamnan na Benue na cikin gwamnonin PDP da suka bayyana a fili sun janye daga yi wa Atiku Abubakar kamfen.

Kara karanta wannan

Muna sane: IGP ya fadi matakin da 'yan sanda ke dauka bisa harin da aka kai kan tawagar Atiku

A yayin da ya ke zargin fulani suka kaiwa mutanen jiharsa hare-hare, Ortom ya ce baya cikin kwamitin kamfen din Atiku.

Don haka, ya ce ba ruwansa da kamfen din har sai Atiku ya bada hakuri kuma ya nuna ra'ayinsa ga jiharsa.

Nyesom Wike

Nyesom Wike
Gwamnonin PDP Da Suka Bayar Da Sharudda A Bainar Jama'a Kafin Yi Wa Atiku Aiki A Jihohinsu. Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya sha alwashin ba zai yi wa dan takarar shugaban kasa na PDPn kamfen ba tunda ya zabi mambobin kwamitin kamfen dinsa a jihar ba tare da tuntubarsa ba, a matsayin gwamna.

Wike ya kuma ce bisa alamu Atiku baya son ya shiga kamfen dinsa. Wike ya yi ikirarin Atiku ya ci mutuncin jihar Rivers kuma ya raina kuri'un da za ta iya kawo wa.

Seyi Makinde

Gwamna Seyi Makinde.
Gwamnonin PDP Da Suka Bayar Da Sharudda A Bainar Jama'a Kafin Yi Wa Atiku Aiki A Jihohinsu. Hoto: Seyi Makinde
Asali: Twitter

Gwamnan na Oyo ya bayyana goyon bayansa ga kungiyar yarbawa ta Afenifere, yayin da kungiyar ta goyi bayan takarar Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC.

Kara karanta wannan

PDP ta tona sirri, ta fadi dalilin da yasa 'yan APC suka farmaki tawagar Atiku a Borno

Makinde, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Bayo Lawal, ya bayyana hakan ne a gidan shugaban Afenifere na kasa, Pa Reuben Fasoranti, a Akure, jihar Ondo.

A baya, gwamnan ya bukaci Atiku ya goyi bayan a mika tikitin takarar shugaban kasa na PDP zuwa kudu, a kudun ma kudu maso yamma, amma dan takarar shugaban kasar bai tanka masa ba.

Gwamnonin G5 Sun Yi Wa Ayu Izgili A Yayin Da Ortom Ya Nada Wa Hanyar Zuwa Gidan Shugaban PDP Sunan Wike

Gwamnoni biyar da ke fushi da shugabannin PDP da aka fi sani da G5, a jiya sun kafa tarihi a Makurdi, babban birnin jihar Benue, a yayin da suka hallarci kaddamar da ayyukan da Samuel Ortom ya fara ya kuma kammala.

A cewar Channels Television, Ortom ya karbi bakuncin Seyi Makinde na jihar Oyo, Nyesom Wike na jihar Ribas, Okezie Ikpeazu na Abia da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa Da Babban Na Hannun Damar Atiku, Wike Ya bayyana Matsayinsa na Karshe Kan Rikicin PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel