Jam'iyyar APC Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Bwacha

Jam'iyyar APC Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Bwacha

  • Kotu ta fitittiki dan takarar kujerar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Taraba, Sanata Emmaneul Bwacha
  • Kotun tarayya ta baiwa hukumar INEC umurnin ta gaggauta shirya sabon zaben fidda gwani
  • Lauyoyin Bwacha sun bayyana cewa zasu daukaka kara ko kuma ayi sabon zaben kawai

Jalingo - Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Jalingo, jihar Taraba ta soke zaben Emmanuel Bwacha a matsayin dan takaran gwamnan jihar na jam'iyyar All Progressives Congress APC.

Soke zaben Bwacha ya biyo karar da daya daga cikin yan takara, David Sabo Kente, ya shigar.

Kotun ta bayyana cewa bisa hujjojin da aka gabatar gabanta, ba'ayi zaben fidda gwani a Taraba ba, rahoton ChannelsTV.

Alkali mai shari'a, Simon Amodeba, ya bada umurnin yin sabon zabe cikin kwanaki 14.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu Ta Zabi Ranar Gardama Tsakanin Gwamnati Da ASUU

Alkali ya umurci Hukumar zabe ta kasa INEC ta soke sunan Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar gwamnan jihar Taraba na jam'iyyar APC.

Bwacha
Jam'iyyar APC Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Bwacha Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkali yace ba zai yiwu mutum daya ya rubuta dukkan sakamakon zaben ba yayinda baturen zaben yace babu zaben da ya gudana a jihar lokacin da aka tsareshi a hedkwatar yan sandan jihar saboda barazanar da ake yiwa rayuwarsa.

Lauyoyi APC da Bwacha sun bayyana cewa zasu karanta shari'a kafin daukaka kara ko kuma su shiga sabon zabe..

Jam'iyyar PDP Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani

A wani labarin kuwa, wata babbar kotun tarayya dake Gusau, jihar Zamfara, ta soke zaben Dauda Lawal a matsayin dan takaran gwamnan jihar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Lawal ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar ne a ranar 25 ga watan Mayu, 2022.

Kara karanta wannan

Taron Gangamin UN: Hotunan Da Bidiyon Shugaba Buhari Yayinda Ya Isa Birnin New York Cikin Dare

Amma a watan Yuni, wasu yan takara hudu suka shigar da kara kotu inda suka bukaci kotu tayi watsi da zaben.

A ranar Juma'a 16 ga Satumba, Alkali Aminu Bappa, ya yanke hukuncin watsi da zaben.

Ya bada umurnin gudanar da sabon zaben fidda gwani idan PDP na son musharaka a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel