Zaben 2023: Gwamnan APC Ya Ce Bai Ma San Wanene Ɗan Takarar Gwamna Na Labour Party A Jiharsa Ba

Zaben 2023: Gwamnan APC Ya Ce Bai Ma San Wanene Ɗan Takarar Gwamna Na Labour Party A Jiharsa Ba

  • Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya ce jam'iyyar Labour Party ba barazana bane ga APC a jiharsa
  • Sule ya yi karin haske da cewa shi kansa bai ma san sunan ainihin dan takarar gwamna na jam'iyyar ta LP a jihar Nasarawa ba
  • Gwamna Sule ya ce dama jam'iyyar ta LP na tunkaho da kungiyoyin kwadago ne amma tuni sun fito sun ce APC suke goyon baya a jiharsa

Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ce bai san wanene dan takarar gwamna na jam'iyyar Labour Party a jihar Nasarawa ba.

Sule ya bayyana hakan ne yayin hirar da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV, rahoton Daily Trust.

Abdullahi Sule
2023: Gwamnan Nasarawa Ya Ce Bai San Wanene Ɗan Takarar Gwamna Na Labour Party A Jiharsa Ba. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Jam'iyyar Labour Party ta fara kamfen na gida zuwa gida a kananan hukumomi 13 da ke jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Daukarwa Al’ummar Kogi Gagarumin Alkawari Gabannin Zaben 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ban wanene ainihin dan takarar gwamna na LP a Nasarawa ba - Gwamna Sule

Da aka masa tambaya ko yana ganin dan takarar gwamna na LP a Nasarawa a matsayin barazana, ya ce:

"Karfin jam'iyyar dama yana tare da kungiyar kwadago ne da kanta, NURTW da sauransu. Ka sani, ba su cikin taron. Sun fito karara sun goyi bayan dan takarar jam'iyyar APC a jihar Nasarawa kuma sun bada dalilansu don haka, ba a gayyace su ba.
"An gayyaci shugabannin kwadago a jihar Nasarawa su ma su je su yi irin wannan wasan kwaikwayon. Sun bi sahun takwarorinsu na jihar Kebbi kuma sun goyi bayan dan takarar APC a Kebbi saboda abin da suka nuna a jihar Nasarawa.
"Don haka babu yadda Labour Party za ta zama barazana ga APC a jihar Nasarawa. Idan za a yi mana barazana, tabbas ba daga Labour Party ba. Maganan gaskiya, ban ma san wanene ainihin dan takarar gwamnan Labour Party ba a jihar Nasarawa kuma ba ba'a na ke ba."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Fitittiki Dan Takaran Gwamnanta A Jihar Ogun Na Jam'iyyar PDP

2023: Nasarar APC Na Cikin Haɗari, In Ji Shugaban Kamfen Na Adamawa

Mataimakin direkta na kungiyoyin tallafi na kwamitin kamfen din yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC a Arewa maso Gabas, Cif Sunny Sylvester Moniedafe, ya ce abin da wasu muhimman masu ruwa da tsaki a jam'iyyar a jihar Adamawa ke yi na barazana ga nasarar ta a babban zaben 2023.

Moniedafe, tsohon mai neman takarar shugaban jam'iyyar APC na kasa ya bayyana hakan ne yayin da ya tattauna da Daily Trust a ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce yan jam'iyyar da ke ganin an zalunce su suna shirin yin yakin neman zabe ba tare da amincewa da Sanata Aisha Binani a matsayin shugaban kwamitin kamfen din shugaban kasa a jihar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel