Kwankwaso Bai Dauko Hayar Kowa Ba, Da Kansa Ya Tsara Manufofinsa Ga Yan Najeriya, NNPP

Kwankwaso Bai Dauko Hayar Kowa Ba, Da Kansa Ya Tsara Manufofinsa Ga Yan Najeriya, NNPP

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, Rabiu Kwankwaso ya gabatarwa yan Najeriya da manufofinsa da ya yi tanadi idan ya gaje Buhari
  • Shugaban jam'iyyar NNPP na kasa, Rufai Ahmed Alkali, ya bayyana cewa Kwankwaso da kansa ya zauna ya rubuta manufofin nasa
  • Alkali ya ce tsohon gwamnan na jihar Kano bai dauko hayar kwararru don rubuta masa manufofin nasa ba don ya shirya lashe zaben shugaban kasa na 2023

Shugaban jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Rabiu Kwankwaso, bai dauko hayar kwararru don su tsara masa manufofinsa ba.

Alkali ya yi jawabi ne a wata hira da Channels TV a ranar Talata, jaridar TheCable ta rahoto.

Rabiu Kwankwaso
Kwankwaso Bai Dauko Hayar Kowa Ba, Da Kansa Ya Tsara Manufofinsa Ga Yan Najeriya, NNPP Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Kwankwaso dai ya gabatar da manufofinsa da ya yiwa yan Najeriya tanadi a ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba a wani taro da aka yi a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Atiku Fa Aikinsa Sayar Da Ruwan Gora, Za Muyi Masa Ritaya Ya Koma Dubai: Kashim Shettima

A taron, Kwankwaso ya ce alkawaran da zai daukarwa yan Najeriya suna kewaye da kudirinsa na son ganin abubuwa sun yiwa kowa daidai a kasar kuma zai yi sa ne don ra'ayin yan Najeriya baki daya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jawabi, Alkali ya ce gabatar da manufofin ya nuna cewa da gaske NNPP da dan takararta na shugaban suke game da lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Alkali ya ce an tsara manufofin Kwankwaso ne don magance damuwa da tsoron yan Najeriya, yana mai cewa takardar cikakkiya ce kuma mai inganci.

Ya ce:

"Ana ta rade-radin cewa NNPP bata dauki zaben 2023 da muhimmanci ba. Akwai kuma rade-radi game da dan takararmu na shugaban kasa da yadda muke abubuwanmu.
"Amma muna ta ba yan Najeriya tabbacin cewa ba za zo wa yan Najeriya a 2023 da abu guda ba- sabon tunani da sabuwar hanyan yin abubuwa ne.

Kara karanta wannan

2023: Gaskiyar Abun da Ke Tsakanina Da Wike, Ortom da Sauran Jiga-Jigan PDP, Peter Obi Ya Fasa Kwai

"Saboda haka, duk abuj da za mu yi dole mu zama masu lissafi, tunani da tsari, kuma an dauki lokaci don samar da wannan takarda sannan a yanzu aka gabatar da shi ga yan Najeriya."

Da yake magana kan nasarorin Kwankwaso, shugaban na NNPP ya yi ikirarin cewa tsohon gwamnan na jihar Kano bai karbi kudin tsaro ba a lokacin da yake matsayin gwamna.

Ya kara da cewar Kwankwaso ya kakkabe dukka basussukan gwamnatin jihar Kano a lokacin da ya zama gwamna sannan bai karbi lowani bashi ba da zai bar kujerar mulki.

Ya kara da cewa

"A gwamnatinsa, bayan bai bar kowani bashi ba, ya kuma bar kudade a asusun gwamnatin jihar lokacin da ya sauka bayan mulkinsa na biyu."

Rabiu Kwankwaso Ya Yi Alkawarin Maida WAEC, NECO, JAMB Kyauta Idan Ya Gaji Buhari

A baya mun ji cewa Rabiu Musa Kwankwaso mai takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP ya nuna gwamnatinsa za ta bada muhimmanci ga ilmi, Punch ta fitar da rahoton nan.

Kara karanta wannan

Rabiu Kwankwaso Ya Yi Alkawarin Maida WAEC, NECO, JAMB Kyauta Idan Ya Gaji Buhari

‘Dan takaran yace zai tabbata daliban Najeriya sun samu damar shiga makarantu gaba da sakandaren kasar nan kyauta, ba tare da sun biya sisin kobo ba.

Kwankwaso yace idan ya yi nasara a 2023, gwamnatinsa za ta cire kudin da ake biya wajen zana jarrabawowi irinsu WAEC, NECO, NBAIS, da kuma NABTEB.

Asali: Legit.ng

Online view pixel