Atiku Fa Aikinsa Sayar Da Ruwan Gora, Za Muyi Masa Ritaya Ya Koma Dubai: Kashim Shettima

Atiku Fa Aikinsa Sayar Da Ruwan Gora, Za Muyi Masa Ritaya Ya Koma Dubai: Kashim Shettima

  • Yakin neman zaben shugabancin kasan Najeriya a 2023 ya dau sabon salo idan Shettima ya caccaki Atiku
  • Tsohon gwamnan na Borno yace shin mutumin da ya gaza hada kan yan jam'iyyarsa ta yaya zai hada kan yan Najeriya
  • Dan takaran shugaban kasan APC ya shirya zama da yan kasuwa masu zaman kansu a jihar Legas

Lagos - Dan takarar kujeran mataimakin shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC ya caccaki dan takaran shugaban kasan PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Shettima a jawabin da ya gabatar a taron tattaunawar Tinubu da yan kasuwa masu zaman kansu a jihar Legas ya bayyana cewa Atiku ruwan gora ya iya sayarwa amma ba wai ya fahimci ilmin tattalin arziki bane.

Ya bayyana cewa gwamnatinsu zata kasance mai girmama doka kuma hakan zai taimakawa yan kasuwa, rahoton ThisDay.

Kara karanta wannan

Addu'a Muke Bukata Daga Amurka Ba Wai Su Tsorata Mu Ba, Ministan Buhari

Yace:

"Habakar tattalin arzikin da muke bukata zai yiwu ne kadai idan muka inganta bangaren shari'a. Zamu tabbatar da ba'a yiwa Alkalai katsalandan don su wanzar da Adalci."
Shettima
Atiku Fa Aikinsa Sayar Da Ruwan Gora, Za Muyi Masa Ritaya Ya Koma Dubai: Kashim Shettima Hoto: Kashim Shettima
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shettima yace Alhaji Atiku Abubakar, kaman Raila Odinga na kasar Kenya ne wanda ya kwashe shekaru yana takarar zabe amma bai taba nasara ba.

Yace:

"Ina ganin girman Atiku, amma shugabanci ba dabara bane. Mutumin da ya kasa hada kan 'yayan jam'iyyarsa shine zai hada kan kasa?"
"Don mutum ya isa sayar da ruwan gora hakan bai nufin masanin tattalin arziki bane. Nan zuwa Mayun shekara mai zuwa zamu yi masa ritayar karshe zuwa Dubai."

2023: Ku kwantar da hankali, za fa ku ci zaben nan, Buhari ga Tinubu da Shettima

A baya mun kawo muku cewa shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja yayin da yake martani ga zabo Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu na zaben 2023 ya kwantarwa da Tinubu hankali.

Kara karanta wannan

2023: Abinda Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Tambayi Kowane Mai Burin Gaje Buhari, Dattawan Arewa

Shugaba Buhari, cikin barkwanci ya ba Tinubu da Shettima kwarin gwiwar lashe zaben shugaban kasa da ke tafe a shekara mai zuwa.

Buhari wanda ya karbi bakuncin dan takarar mataimakin shugaban kasa jim kadan bayan shugabannin APC da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu sun kaddamar dashi, ya ce ya yi matukar farin ciki da zabo tsohon gwamnan na jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel