Buba Galadima: Kwankwaso Zai Kawo Dukkan Jihohin Arewa a 2023

Buba Galadima: Kwankwaso Zai Kawo Dukkan Jihohin Arewa a 2023

  • Tsohon makusancin shugaban kasa Muhammadu Buhar, Buba Galadima, ya bayyana cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai kawo dukkan jihohin arewa
  • Galadima ya sanar da cewa, Kwankwaso zai kawo hatta jihohin da abokan hamayyar Kwankwaso ke rike da ita a zaben 2023 mai gabatowa
  • Ya sanar da cewa, a kalla Kwankwaso zai kawo kuri’u sama da miliyan hamsin a jihohin arewa kadai, don haka zai shugabanci Najeriya

Buba Galadima, tsohon mamba a kwamitin yardaddu na jam’iyyar APC, yace Rabiu Kwankwaso ne zai lashe zabe a dukkan jihohin arewa a zaben shugabancin kasa na 2023 dake zuwa.

Kwankwaso
Buba Galadima: Kwankwaso Zai Kawo Dukkan Jihohin Arewa a 2023. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Kwankwaso shi ne ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar NNPP mai alamar abarba, The Cable ta rahoto.

A yayin jawabi a ranar Alhamis a tattaunawarsa da Channels TV, Galadima yace Kwankwaso zai lashe zabe a shiyoyi uku na arewa kuma ya samu kuri’u a inda abokan hamayyarsa ke da karfi.

Kara karanta wannan

NNPP ta fadi dalilan da suka sa Kwankwaso ya ki martaba gayyatar dattawan Arewa

“PDP bata kan takardar kada kuri’a saboda karfi ta a kudu maso gabas ne wanda kuma Peter Obi suke yi. Wurin da PDP ke da karfi kuma shi ne kudu kudu. Kamar yadda Wike baya goyon bayan Atiku, kudu kudu ta kubuce masa.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

- Yace.

“Arewa dukkanta ta Kwankwaso ce saboda ya kawo Taraba, Adamawa, Gombe da Bauchi wanda ya hada da gwamnoninsu.
“Zai yi nasara a arewa maso gabas, arewa ta tsakiya kuma ya kawo arewa maso yamma. Idan aka hada duka, zasu samu kuri’u sama da miliyan hamsin.
“Kwankwaso zai samu wani kaso a kudu kudu, kudu maso gabas da kudu maso yamma.
“Ina gabatarwa da dukkan ‘yan Najeriya dake bukatar ‘yanci, cigaba da kiwon lafiya mai daurewa, cewa basu da wani da ya dace su zaba baya da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.”

Kara karanta wannan

Anambra da Jihohi 7 da Peter Obi Zai Iya Yi wa Atiku Lahani a Zaben Shugaban kasa

Tinubu da Na Son Kai, Ba Zan Zabe Shi Ba a Zaben 2023, in Ji Farfesa Akintoye

A wani labari na daban, Gabanin zaben 2023 na shugaban kasa, farfesa Banji Akintoye, shugaban kungiyar Yarbawa ta Yoruba Nation Self-Determination Struggle ya bayyana kadan daga halin dan takarar shugaban kasa na APC.

Ya kuma bayyana cewa, tabbas ba zai zabi Bola Ahmad Tinubu ba saboda wasu dalilai da ya bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel