Yanzu-Yanzu: Zababben Gwamnan Ekiti Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki

Yanzu-Yanzu: Zababben Gwamnan Ekiti Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki

  • A yau Lahadi 16 ga watan Oktoba, 2022 aka rantsar da sabon zababben gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji a gaban dandazon mutane
  • Manyan kusoshin jam'iyyar APC sun halarci wurin taron ciki har da dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
  • Gwamna Oyebanji ya karbi mulki hannun tsohon gwamna, Kayode Fayemi, wanda ya rike shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya

Ekiti - Mista Biodun Oyebanji ya karbi shahadar kama aiki a matsayin zababben gwamnan jihar Ekiti na biyar a mulkin demokaraɗiyya.

Oyebanji ya gaji tsohon gwamna, Kayode Fayemi, wanda ya yi aiki a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF).

Gwamna Biodun Oyebanji.
Yanzu-Yanzu: Zababben Gwamnan Ekiti Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki Hoto: Biodun Oyebanji
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an rantsar da Oyebanji tare da mataimakiyarsa, Chief Monisade Afuye, a Ekiti Parapo Pavillon, Ado-Ekiti, babban birnin jihar yau Lahadi, 16 ga watan Oktoba, 2022.

Babban Alkalin jihar Ekiti, Mai shari'a Ayewole Adeyeye, shi ne ya bai wa sabon gwamnan rantsuwar shiga Ofis da misalin karfe 12:52 a gaban dandazon mutane.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamnan APC Ya Yi Muhimman Naɗe-Naɗe Biyu, Ya Umarci a Garkame Asusun Gwamnati

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hotunan wurin taron

Sabon gwamnan jihar Ekiti.
Yanzu-Yanzu: Zababben Gwamnan Ekiti Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki Hoto: Biodun Oyebanji
Asali: Facebook

wurin rantsar sa sabon gwamnan Ekiti.
Yanzu-Yanzu: Zababben Gwamnan Ekiti Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki Hoto: Ekiti State
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya halarci wurin taron.
Yanzu-Yanzu: Zababben Gwamnan Ekiti Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki Hoto: Bola Tinubu
Asali: Facebook

Wurin Taro.
Yanzu-Yanzu: Zababben Gwamnan Ekiti Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki Hoto: Ekiti State News/facebook
Asali: Facebook

Manyan jiga-jigan siyasar kasar nan sun halarci wurin taron rantsarwan ciki har da ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.

A wani labarin kuma Bayan Tawagar Wike, Wasu Gwamnonin PDP Hudu Sun Yi Barazanar Watsi da Atiku a 2023

Rikicin jam'iyyar PDP ya sake ɗaukar sabon babi yayin da wasu gwamnoni hudu suka haɗa kai don yakar Wike da makusantansa.

Gwamnonin sun yi barazanar janye wa daga kamfen Atiku idan har ya rasa mafita kuma ya sa Ayu ya yi murabus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel