Sabon Gwamnan Jihar Ekiti Ya Yi Muhimman Nade-Nade Biyu Na Farko, Ya Kulle Asusu

Sabon Gwamnan Jihar Ekiti Ya Yi Muhimman Nade-Nade Biyu Na Farko, Ya Kulle Asusu

  • Gwamanan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya naɗa mutum biyu karon farko bayan shiga Ofis a matsayin sabon gwamna ranar Lahadi
  • Gwamnan ya naɗa Mace kuma Musulma, Habibat Adubairo, a matsayin sakatariyar gwamnatinsa
  • Ya kuma naɗa Sakataren watsa labarai sannan ya ba da umarnin kulle dukkanin asusun gwmanatin Ekiti

Ekiti - Sabon gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya naɗa Dakta Habibat Adubiaro, a matsayin Sakatariyar gwamnatin jiha, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Gwamna Oyebanji ya kuma amince da naɗin Mista Yinka Oyebode, a matsayin Sakataren watsa labarai (CPS).

Gwamna Biodun Oyebanji, na jihar Ekiti.
Sabon Gwamnan Jihar Ekiti Ya Yi Muhimman Nade-Nade Biyu Na Farko, Ya Kulle Asusu Hoto: Biodun Oyebanji.
Asali: Facebook

Wannan na kunshe a wasu sanarwa guda biyu daban-daban masu ɗauke da sa hannun shugaban ma'aikata, Mista Bamidele Agbede, ranar Lahadi jim kaɗan bayan rantsar da shi.

Naɗin guda biyu, a cewar sabon gwamnan da ya kama aiki ranar 16 ga watan Oktoba, 2022, zasu fara aiki ne nan take ba da ɓata lokaci ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Habibat Adubiaro, cikakkiyar Musulma, ta yi aiki a matsayin mai ba da shawara ta musamman a zangon farko na mulkin tsohon gwamna Ayodele Fayose.

A halin yanzun ita ce shugabar ƙungiyar mata musulmai ta ƙasa reshen jihar Ekiti, 'Federation of Muslim Women’s Association of Nigeria.'

A ɗaya bangaren kuma, Mista Oyebode ɗan asalin garin Ido Ile, ƙaramar hukkumar Ekiti ta yamma, a zangon mulkin farko na gwamna Fayemi aka naɗa shi babban mai taimaka wa kan harkokin yaɗa labarai daga bisani aka mai da shi CPS.

Fayemi ya sake naɗa Oyebode a wannan muƙami bayan ya dawo zango na biyu a 2018 kuma ya yi aiki har zuwa ranar karshe gabanin gwamna Oyebanji ya sabunta naɗa shi a muƙamin.

Sabon Gwamnan ya rufe Asusun gwamnati

Bayan naɗe-naɗen kuma, gwamna Oyebanji, ya ba da umarnin garkame dukkanin asusun gwamnati har sai baba ta gani.

A wata sanarwa da sakataren watsa labarai, Yinka Oyebode, ya fitar, gwamnan ya umarci kowane Akanta ya bi wannan umarnin nan take.

A wani labarin kuma Manyan Alkawurra Uku da Atiku Ya Daukar Wa Jagororin Arewa a Kaduna

Atiku Abubakar ya yi alkawarin magance matsalar tsaro da ya addabi yankin arewa idan ya ɗare shugaban kasa a 2023.

Ɗan takarar kujera lamba ɗaya a inuwar PDP yace ya shirya tsaf wajen tsamo tattalin arzikin kasar nan daga durkushe wa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel