Da Duminsa: Kotu ta Fatattaki Aishatu Binani Matsayin ‘Yar Takarar Gwamna a APC a Adamawa

Da Duminsa: Kotu ta Fatattaki Aishatu Binani Matsayin ‘Yar Takarar Gwamna a APC a Adamawa

  • Babbar kotun tarayya dake zama a Yola jihar Adamawa ta soke zaben fidda gwani Na takarar kujerar gwamna a jam’iyyar APC
  • Kotun ta soke halaccin Sanata Aishatu Binani matsayin ‘yar takarar gwamnan Adamawa a karkashin jam’iyyar APC a Adamawa
  • Kamar yadda alkalin ya bayyana, APC bata da ‘dan takarar Gwamna a Adamawa a zaben 2023 mai gabatowa

Adamawa - Wata babbar kotun tarayya dake zama a Yola ta soke zaben fidda gwani na kujerar Gwamnan APC na jihar Adamawa wanda ya samar da Aishatu Binani matsayin ‘yar takarar kujerar Gwamnan jihar a jam’iyyar, Channels TV ta rahoto.

Kotun a ranar Juma’a ta bayyana cewa jam’iyyar APC bata da ‘dan takarar kujerar Gwamna a jihar a zaben 2023 mai gabatowa amma tace daga mai kara har wanda aka yi kara suna da damar daukaka kara.

Karin bayani na nan tafe…

Asali: Legit.ng

Online view pixel